Buhari Zai Gina Sabbin Gidajen Yari Guda 6 A Najeriya

183

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta gina sabbin gidajen gyaran hali guda shida a shiyyoyin siyasa shida dake Najeriya.

Ministocin Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka ranar Asabar a lokacin da yake duba aikin ginin sabon gidan gyaran hali da Gwamnatin Tarayya take ginawa a Janguza dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Mista Aregbesola ya ce gina sabon gidan gyaran halin yana daga cikin aikace-aikace da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro da su don kawo gyara a gidajen gyaran hali na Najeriya.

“Muna nan muna jajircewa don kawo gyara a gidajen gyaran halin da muke da su a Najeriya.

“Abin da muke da shi a nan misali ne na abin da muke so mu samu a dukkan faɗin ƙasar nan, kuma wannan yana cin mutum 3000, kuma muna shirin gina irin sa a dukkan shiyyoyin siyasa shida.

“Wannan ya fi ci gaba ta fuskar faɗi da sauran kayayyaki. An tsara shi ne ga mazauna gidajen gyaran hali masu jiran shari’a, masu buƙatar tsaro kaɗan, masu buƙatar matsakaicin tsaro da masu buƙatar tsaro mai yawa.

“Hanyar shigowa wannan gida da nagartar aikin sun birge ni sosai”, in ji shi.

Mista Aregbesola ya yaba wa Shugaba Buhari bisa irin goyon bayan da yake bayarwa a ta fannin kawo gyara a gidajen gyaran hali.

A jawabinsa, Ahmad Jafaru, Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, NCoS, ya ce sabon gidan gyaran halin na Janguza yana ɗauke da ɗakunan girki, makaranta, asibiti, cibiyar koyon sana’a da kuma masallaci.

Ahmad ya ce an tsara ƙaddamar da gidan gyaran halin a wannan shekara, yana mai ƙarawa da cewa tuni NCS ta ɗaga darajar tsohon Gidan Gyaran Yari na Kurmawa zuwa cibiyar gyaran hali.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya bada rahoton cewa Minista Aregbesola ya samu rakiyar Shugabannin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, NIS, Hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps, NSCDC da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan