Home / Addini / Jahilai ne ke sukar fatawar Sheikh Bashir Aliyu Umar kan sakin aure a film – Sheikh Umar Sani Fagge

Jahilai ne ke sukar fatawar Sheikh Bashir Aliyu Umar kan sakin aure a film – Sheikh Umar Sani Fagge

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke jihar Kano, Sheikh Umar Sani Fagge, ya ce marasa Ilimi ne ke sukar fatawar da Dakta Bashir Aliyu Umar ya yi akan duk wanda ya saki matarsa a cikin shirin film to ta gida ta saku.

Sheikh Umar Sani Fagge ya yi wannan bayanine ta cikin wani fai-fafan bidiyo mai munti 1:30 da aka wallafa a shafin facebook ranar Litinin.

Haka kuma Sheikh Umar Sani Fagge ya ce duk wanda ya soki fatawar Dakta Bashir Aliyu Umar to ya nuna baya karatu kuma bai san darajar malanta ba.

Sheikh Umar Sani Fagge

Idan za a iya tunawa dai Dakta Bashir Aliyu Umar da ke zaman babban limanin masallacin juma’a na Alfurqan ya ce duk wanda ya saki mace a cikin shirin film to dai-dai yake da sakin matarsa ta gida.

Shehin malamin ya ce duk wani danwasa da ya furtawa matarsa ta film saki, to ba bu shakka ya saki matarsa ta gida, kuma babu aure a tsakaninsu.

“Ko da wasa idan kazo aka daura maka aure a film, mutum ya ce ya saki matansa kuma yana da mata, kuma ya fada ya ce ai matan nawa duk na sake su, wai yana nufin matansa na wasan Hausa, to na gasken sun tafi.

“Ba a wasa da sha’anin saki, ko kuma aure, kazo a cikin wasan Hausa a ce an daura maka aure, sannan kace kuma wannan ba aure ba ne? kuma an daura aure an cika sharadan aure, to aure ya dauro.

To sai dai wannan fatawa bata yiwa jama’a da dama dadiba, musamman masu sana’ar film.

Hakance ta sanya jama’a suka fara surutai da sukar malamin a shafukan sada zumunta na facebook da sauransu.

Sai dai Malam Umar Sani Fagge ya fito ya baiwa malamin kariya, inda ya ce fatawarsa na kan dai-dai.

Har ma ya kawo hadisai da suka dace da fatawar, inda ya ce bisa doron hadisin, saki baya la’akari da niyya, indai anyishi ko da wasa to ya tabbata.

Kano Focus

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

2 comments

  1. Muna Mika sakon gaisuwa zuwa ga malamanmu Allah ya Kara baiwa da hazaka da tunani da ilimi Mai amfani

  2. Allah ya karawa malam Lfy, da nisan kwana Mai anfani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *