Ƙungiyar Kwankwasiyya Bala’i ce kuma Asara ce – Gwamna Ganduje

387

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ƙungiyar Kwankwasiyya Bala’i ce kuma ƴan ƙungiyar daƙiƙai ne domin ƙwaƙwalwarsu ba ta ja.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a wata muryar mai tsahon daƙiƙa 24 da ke yawo a shafukan Intanet, wanda da alama an ɗauki muryar ne a gurin taron siyasa.

Babu shakka Kwankwasiyya asara ce, ƙungiyar Kwankwasiyya Bala’i ne, Ƙungiyar Kwankwasiyya Hauka ne, kuma daƙiƙai ne domin kan su ba ya ja, ƙwaƙwalwar su ta jaki ce” In ji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa kuma gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje sun kwashe shekaru huɗu suna jan ragamar jihar Kano wato daga shekarar 1999 zuwa 2003, kafin gwamna Ibrahim Shekarau ya kayar da su.

Bayan faduwarsu a neman tazarce, mutanen biyu sun kwashe shekaru kimanin 8 suna aiki tare a gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, kafin 2011 lokacin da suka sake samun nasara suka yi dawayya kan karaga.

Haka kuma a cikin shekarar 2015 ne kuma Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ɗaga hannun Ganduje inda ya zama gwamnan jihar Kano, amma shekara ɗaya bayan nan ne rashin jituwa tsakanin abokan siyasar biyu ta kunno kai har zuwa shekarar 2019, wani lokaci da rikicin ya fi ta’azzara.

Kungiyar Kwankwasiyya dai ta yi suna sosai a faɗin Najeriya, inda magoya bayan tsohon gwamnan kuma tsohon Sanata na mazabar Kano ta Tsakiya, ke tawassali da irin ayyukan ci gaba da su ka ce shugaban nasu ya yi a wancan lokacin, domin kafa hujjar farin jinin da kungiyar take da shi a fagen siyasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan