Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci ma’aikata da su zauna a gida

364

Sakamakon ƙaruwar masu ɗauke da cutar Korona Gwamnatin jihar ta umarci ma’aikata a jihar da su zauna a gida, cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a safiyar yau Talata.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan zama na musamman da masu ruwa da tsaki akan harkar lafiya a jihar Kano, a ƙarshe Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da rufe gidajen kallo da gidajen bukukuwa da sauran guraren taruwar jama’a.

Wannan sanarwar na zuwa ne kwana ɗaya da aka dawo makaranta a mafi yawan jihohin ƙasar nan.


Haka kuma a ɗan tsakanin ana yawan samun ƙaruwar alƙaluman masu ɗauke da cutar Korona, kamar yadda hukumar hana yaɗuwar cutttuka ta ƙasa NCDC ke fitarwa a kowacce rana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan