Najeriya za ta samar da allurar riga-kafin cutar Korona – Ministan Lafiya

200

Ma’aikatar Lafiya ta ƙasa ta saki naira biliyan 10 kwatankwacin dala miliyan 25 domin samar da allurar riga-kafin annobar korona ta cikin gida.

Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ne ya sanar da hakan yayin jawabin da kwamitin shugaban kasa mai yaki da annobar korona ya yi a jiya Litinin.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da alkaluman annobar ta korona ke ci gaba da dagawa a faɗin Najeriya.

Ministan na Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce fitar da wannan kudi domin samar da allurar rigakafi ‘yar gida domin dakile wannan annoba ya zama dole.

Sai dai ya kara da cewa duk da yunkurin gwamnati na samar da rigakafin ‘yar gida to ƙasar nan za ta cigaba da nema daga kasar waje kasancewar akwa al’umma mai dimbin yawa a ƙasar nan.

Dr Osagie ya kuma ce tuni hukumomi a ƙasar nan su ka fara neman iznin samar da rigakafin da za ta karbu a duniya, ta hanyar aiki tare da cibiyoyin da kamfanonin magungunan da aka amince da su.

Ministan lafiyar ya yi amfani da damar da ya samu wajen yin kira da ‘yan Najeriya su yi watsi da yaudarar da ake yi musu cewa a yanzu haka akwai allurar rigakafin annobar ta siyarwa, inda bayyana al’amarin da damfara.

Dangane kuma girman annobar korona a Najeriya a yanzu haka, minister Osagie ya ce dole ne jama’a su yi taka tsan-tsan kasancewar cutar ta yi wa kasar kome da karfi.

” A makon da ya gabata, kusan a duk mutum biyar da aka yi wa gwaji akwai mutum daya mai dauke da kwayar cutar ta korona sannan kuma ta yi ajalin mutum 77 a makon.”

Watakila wannan shiri na gwamnatin Najeriya ya kwantarwa da wasu ‘yan kasar nan hankali dangane da ke da shakkun da suke da shi kan allurar rigakafin cutar korona ‘yar waje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan