Sukar Ganduje akan zaɓen ƙananan hukumomi rashin adalci ne – Nasiru Zango

235

Fitaccen ɗan jaridar da ke aiki da gidan rediyon Freedom da ke jihar Kano, Nasiru Salisu Zango, ya ƙalubalanci masu ganin baiken gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, akan zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a ƙarshen makon jiya.

Nasiru Salisu Zango ya yi wannan furucin ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na facebook mai takenBabu wani aibu a zaɓen ƙananan hukumomi na Kano’
Nasiru Zango ya ce “Bisa yadda zaɓen ƙananan hukumomi ya gabata A Kano, sakamakon zaɓen bai kamata ya ɓatawa mai hankali rai ba, kuma duk wanda ya soki gwamna Ganduje akan yadda zaɓen ya gudana bai yi adalci ba, domin ba kan sa ne farau ba, shirya maguɗi da jirga nasara ga jami’iyya mai mulki a irin wannan zaɓe, dan haka ni a ra’ayi na mai girma gwamna ya daɓɓaka sunnar zaɓukan ƙananan hukumomi ne ta ƙasar nan”

Ya ƙara da cewa “Mafi akasarin gwamnonin ƙasar nan abin da su ke so shi ake rubatawa idan zaɓen ƙananan hukumomin ya zo dan haka bai kamata a yi mamaki domin shi ma gwamna Ganduje ya mori wannan dama da dukkan gwamnonin ke amfani da ita ba”

Dan jaridar ya ce “Idan ana son gyara daga tushe za’a ɗauko shi a kakkaɓe duk wata dama da ke baiwa masu mulki damar tafka magudi a zabe, idan ko ba a yi haka ba to fa dole kullum abin gaba zai ta yi”

Hakazalika Nasiru Salisu Zango ya ce “Ni abin dake so sa min rai shi ne kashe kuɗaɗen al’umma akan abin da kowa ya san gidoga ce, maimakon haka kyautuwa yayi a baiwa gwamnoni dama su ringa naɗa shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, kaga shike nan an yi abin a zahiri maimakon cikin dabaru da ake yi a yanzu”

A ƙarshe ya ce “Ina taya dukkan shugabannin da suka lashe wannan zaɓe murna ina fatan Allah yasa su gama lafiya. Shi kuma tsarin mu da kullum yake mai damu baya ina rokon Allah ya bamu ikon zaɓo waɗanda za su zo su gyara mana”

A ranar Asabar ɗin makon jiya ne hukumar zaɓe ta jihar Kano KANSIEC ta shirya zaɓen ƙananan hukumomi a jihar, inda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaɓen gaba ɗayansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan