Tsadar ‘Man Gyaɗa’ a Kano ta haifar da hauhawar farashin Ƙosai da Awara

308

Hauhawar farashin man gyada a jihar Kano ya sabba karuwar farashin kosai da awara da sauran kayan da ake sarrafawa da man gyada.

A ƴan kwanakin nan ƙosai da awara da fanke sun yi tashi gwauron zabo sakamakon karuwar farashin man gyada a fadin jihar.

Binciken da jaridar Kano Focus ta gudanar ya gano cewar a baya dai ana sayar da kwalbar man gyaɗa akan Naira 450, da a yanzu kuma ake sayarda kowacce kwalba akan Naira 650 zuwa Naira 700.

Hakazalika a yanzu ana sayar da karamin galan akan Naira 5500, sabanin yadda ake sayar dashi a baya da bai gaza Naira 300 ba.

Kosai Naira 10 Duk Guda Ɗaya

Hajiya Aisha Sulaiman wata mai sana’ar tuyar kosai ce a birnin Kano, ta ce ya zama dole ta mayar da sakin kosai daga Naira 5 zuwa Naira 10 sakamakon tsadar da man gyadar yayi.

A cewarta matukar bata ƙara farashin ba to ba za ta iya mayar da kudin da ta kashe ba ballantana ta ci riba.

“Ya zama dole nayi hakan, idan ba haka ba ba zan mayar da kudina ba.

“Wake ya yi tsada, muna siyan kwano akan Naira 800 ga kuma mai shima yadda kullum yake ƙara kuɗi.

“Mankuli ma ana saida shi ne akan Naira 800, to ka ga ba mu da zabi tun da ba za mu yi tuya da manja ba.” a cewar ta.

Biyu 50 Muke Sayar Da Fanke

Ita ma Ruƙayya Muhammad da ke zaune a unguwar Tukuntawa da ke sana’ar tuyar fanke ta ce kafin ƙaruwar farashin mangyadar tana sayar da fankenta akan naira goma duk guda ɗaya.

Sai dai ta ce a yanzu dole ya sanya take sayarwa akan Naira 50 duk guda biyu.

Ta ce duk da ta kara kudin amma mutane na cigaba da zuwa siya sai dai ba kamar a baya ba, lokacin da take sayarwa akan Naira 10.

“Ni kaga jarka nake siya amma wallahi a hakan ma da kyar nake mayar da kudi na, kaima dai kasan yadda abubuwa suke tsada kulllum abubuwan ƙara kudi suke yi.

“Wasu idan suka zo siya dana faɗa musu yadda na koma siyarwa sai su yi tafiyar su, ba sa dawowa, don ranar da na fara canza farashi ma sai da nayi kwantai,” a cewar ta.

Mun Fi Sayar Da Awara Akan Uku Naira 50

Talatu Gambo da ke sana’ar Awara akan titin Gidan Zoo ta ce duk da kuɗin Wake ya ƙaru amma tana siyar da Awararta duk guda daya akan naira goma.

Sai dai ta ce a yanzu da farashin mangyada ya karu ta koma siyarwa akan guda uku naira hamsin.

“Saboda a gefen titi nake ciniki, shiyasa koda na sauya farashi ana cigaba da siya,

“Haka kuma ko yanzu farashin ya ragu to nima zan rage nawa farashin ya koma kamar da.

“Ni dai dana tambaya meyasa kudin mangyadan ya karu sai aka cemin wai yanzu ba a noma gyada, a kasar nan yawanci ana kawo ta ne daga Senegal,” a cewar ta.

Ina Makomar Jama’a?

Jama’a da dama da aka zanta da su kan wannan ƙari da aka samu, sun nuna rashin jin dadinsu da halin da aka tsinci kai a ciki.

Wani matashi mai suna Ibrahim Isma’il da ke kan layin siyan ƙosai ya ce kwanaki uku da suka gabata Nair 5 ya sayi ƙosan duk guda ɗaya sai dai yanzu ya koma Naira 10.

“Kwana uku da nazo na siyi kosai duk daya Naira 5, amma a yau da na dawo ana sai da guda daya Naira 10.

Haka na haƙura na siya saboda iyalina ta damamin koko kuma ba zai shawu ba babu kosai.

“A da ina siyan na Naira 200 amma yau sai da na siyi na Naira 500 saboda farashi ya tashi.” inji Ibrahim Isma’il.

Abubakar Abdulaziz da shi ma da ya je siyan ƙosai cewa ya yi ba zai iya siyan kosai ba a halin yanzu, duba da yadda aka ƙara masa kuɗi.

Ya ce a da yana siyan na dari da hamsin ne wanda ake bashi duk guda daya a Naira 5 saɓanin yanzu da aka ce masa Naira 10.

Ko Hakan Ya Shafi Mata A Gida?

Sadiya Hassan uwargida ce da ke zaune a unguwar Tukuntawa ta ce a yanzu ba a samun man gyada na Nair 50 saɓanin yadda a baya ake basu

“A watannin baya Naira 50 ko Naira 100 ta isheni nayi miyar kuka ko miyar shinkafa, amma yanzu sai na saka Naira 150 na ke iya siyan man da zan yi girki dashi.

“Kuma kudin cefanen da ake bamu ba karuwa yayi ba, a haka muke riritawa mu girka koda babu dadi don girki ba zai yiwu ba idan babu mai, shi kansa yanzu manjan tsada yake yi,” inji Sadiyya.

Jamila Muhammad cewa ta yi a yanzu suna yin girkine kawai da hikimomi tunda dai abubuwa sun ta’azzara.

“Gaskiya ni kaga mai gidana baya son girki da manja, kuma yanzu mangyadan ya yi tsada, hakuri kawai ake yi, ni a yanzu ma nafi jiƙa garin kwaki musha da yarana, saboda tsadar da man yayi,” a cewar ta

Ko Me Dillalan Man Ke Cewa?

Abdullahi Adamu da ke sana’ar sayar da mangyada a kasauwar Rimi ya ce watanni biyu da suka gabata suna siyar da mangyada duro guda akan Naira 170,000, amma a yanzu suna sayarwa ne aka Naira 190,000.

Ya kuma ce suna sayarda yaluwar jarka akan Naira 19,500, sai kuma ƙaramin galan suna sayarwa akan Naira 4000 sai kuma kwalba ɗaya akan Naira 650.

Ya kuma ce tashina man na da nasaba da gyadar da ake sarrafawa domin yin mangyadar, ana shigo da ita ne daga ƙasashen ketare.

A cewarsa hakan ya farune sakamakon ƙarancin noman gyaɗa a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Sai dai ya ce farashin yana hawa da sauka ne a galibin lokuta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan