Home / Ilimi / Wuraren Da Ake Amfani Da Babban Baƙi A Rubutun Hausa— Daga Muhammad Sabi’u

Wuraren Da Ake Amfani Da Babban Baƙi A Rubutun Hausa— Daga Muhammad Sabi’u

A wannan kafar, kullum muna ƙoƙari wajen ganin mun inganta rubutun Hausa da jama’a suke yi a kafafen sadar da zumunta da sauran wuraren da suke rubutu da harshen Hausa. Kamar yadda Turanci yake, haka harshen Hausa ma yake. Kowanne yana da ƙa’idojinsa. A wasu wuraren kuma, ƙa’idojin harsuna biyun sukan yi kama da juna. Misali, a harshen Hausa, akwai wasu ƙa’idojin rubutun da a wajen Turanci ya aro su.

A yau kuma muna son yin magana ne game da girmama baƙi a rubutu. Wannan ƙa’idar ma, a wajen Turanci aka aro ta.

Da farko tukuna, mene ne girmama baƙi? Girmama baƙi wata dabarar rubutu ce da ake amfani da babban harafi wajen rubuta harafin farko na kalma. Yawanci harafin da ya zo a farko shi ne ake fara mayar da shi babban baƙi.

Ana amfani da babban baƙi ne wajen rubuta sunan yanka: sunan mutum, addini, ƙabila, gari, jiha, ƙasa, nahiya da sauransu. Misali, idan mutum zai rubuta Musa, Fatima, Ado, Birtaniya, Najeriya, Afirka, Turai, Musulunci, Kiristanci, ba zai fara rubuta su da ƙaramin baƙi ba. Me ya sa? Saboda dukkansu sunayen yanka ne. Haka ake rubuta su ko da ba a farkon jimla suka fito ba.

Duba waɗannan misalan a cikin jimla:
1A. Ni musulmi ne (kuskure).
1B. Ni Musulmi ne (daidai).
2A. Daga najeriya nake (kuskure).
2B. Daga Najeriya nake (daidai).
3A. Na aiki fatima gida (kuskure).
3B. Na aiki Fatima gida (daidai).

About Hassan Hamza

Check Also

Mun Buɗe Cibiyoyin Rijista Na Bogi Don Mu Kama Masu Satar Jarrabawa— JAMB

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB, ta kafa abin da ta …

One comment

  1. Allah yayi muku albarka ka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *