Gwamnatin jihar Kano ba ta da niyyar cefanar da gidan ‘Marayu’ – Zahra’u Muhammad

228

Kwamishiniyar ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta bayyana gwamnatin jihar ba t da niyya ko ƙudurin sayar da gidan Marayu da ke yankin unguwar Nasarawa, a cikin birnin Kano.

Dakta Zahra’u Muhammad ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’ar yaɗa labarai ta ma’aikatar, Bahijja Malam Kabara ta fitar tare da rabawa manema labarai.

Kwamishiniyar ta ce gwamnatin Kano da ma’aikatar mata da walwalar jama’a ce ta ga ya dace ta ɗebi wasu daga cikin yaran da su ke gidan Marayu na Nasarawa zuwa wani sabon gidan marayun da aka gina a garin Gaya, a matsayin gwaji a maimakon a bar sabon gidan marayun da aka gina ya lalace.

A ƙarshe Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da dukkanin wata jita – jita a gane da wannan batun.

Al’ummar jihar Kano dai na ci gaba da tafka muhawara game da zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cefanar da wasu daga cikin ƙadarorin gwamnatin jihar.

Sai dai Gwamna Ganduje da Kwamishinansa na yaɗa labarai Muhammad Garba na fitowa akai-akai suna cewa ba sayar da wuraren ake yi ba, ana ba da su ne ga masu bunƙasa birane zuwa wasu ‘yan shekaru kafin daga bisani su koma ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar ta Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan