Home / Addini / Mun yaba da ayyuka da ƙoƙarin jaridar Labarai24 – Hukumar Hisbah

Mun yaba da ayyuka da ƙoƙarin jaridar Labarai24 – Hukumar Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta yaba da irin ayyuka da ƙoƙarin da fitacciyar jaridar nan da ke yaɗa labaran ta a shafukan Intanet da harshen Hausa, wato Labarai24.

Babban kwamandan Hisbar, Ustaz Muhammad Harun Ibn Sina ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke karɓar wakilcin hukumar gudanarwar jaridar ta Labarai24 a ofishinsa da ke birnin Kano.

Ustaz Harun Ibn Sina ya ƙara da cewa jaridar Labarai24 ita ce jarida ta farko wacce ta ke yaɗa labaran ta a shafukan Intanet, da ta fara kawo masa irin wannan ziyarar. Ya kuma ce za su yi aiki kafaɗa – da – kafaɗa wajen yin aiki tare da wannan jarida ta Labarai24.

Ma’aikatan Jaridar Labarai24 da Kwamandan Hisba na jihar Kano

Hakazalika, Kwamandan Hisbar ya ce hukumar Hisbah tana matuƙar jin dadi akan yadda jaridar Labarai24 ke yaɗa labaran da su ka shafi hukumar.

A nasa ɓangaren babban Editan kuma mawallafin jaridar Labarai24 Abubakar Sulaiman (SD), wanda ya samu wakilcin Malam Habeeb Shareef, ya bayyana godiyarsa da irin tarbar da babban kwamandan Hisbar ya yi musu.

Habeeb Shareef ya kuma sha alwashin cewa jaridar za ta cigaba da yaɗa labaran na hukumar Hisba da kuma sauran ingantattun labarai masu tushe.

Ustaz Harun Ibn Sina, Habeeb Shareef da wasu daga cikin ma’aikatan Labarai24

A ƙarshe babban kwamandan Hisbar ya ce ƙofar hukumar ta su a buɗe ta ke wajen yin aiki tare da jaridar Labarai24, domin tuni sun samu sahhalewa daga ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano, wajen yin aiki da shafukan jaridun Intanet, tare da buɗe shafin yanar gizo mallakin hukumar.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *