Muna samun yawan ƙorafi akan yadda Mazan Kano ke dukan Matansu – Hisba

212

Babban kwamandan Hisba na jihar Kano Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, ya bayyana cewa a ɗan wannan tsakanin hukumarsa tana yawan karɓar ƙorafi daga matan aure akan yadda mazajensu ke dukansu.

Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina ya ce a ƴan kwanakin nan kullum sai sun samu ƙorafin yadda maza ke dukan matansu a Kano. Ya ƙara da cewa duk da cewa dukan da Mazan ke yiwa Matan ba wani mai yawa ba ne, amma ya kan haifar da babbar illah ga lafiyar matan.

Babban kwamandan Hisbar ya ce a lokutan baya hukumar ta fi karɓar ƙorafin yadda Mata ke halaka Mazajensu ta hanyar daɓa musu wuƙa, amma yanzu abin ya canza domin sun fi samun ƙorafi akan dukan Mata da Mazaje ke yi wanda hakan kan haifar musu da lahani.

Hakazalika, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, ya ce a cikin mako ɗaya kacal sun karɓi ƙorafin dukan Mata guda goma.

A ƙarshe Muhammad Harun Ibn Sina ya ja hankalin al’umma da su zauna da matansu lafiya domin zaman lafiya shi ne ginshiƙin cigaban rayuwa, kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yana yin hani da dukan Mata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan