Home / Labarai / Wani matashi ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda gaza biyan bashi a Kano

Wani matashi ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda gaza biyan bashi a Kano

A wani al’amari mai kama da almara domin kuwa wani matashi ne mai suna Surajo Dauda ya hadiyi zuciya ya mutu saboda gaza biyan bashin da ake binsa.

Tun da farko wani mai suna Mustapha B Mustapha ne ke bin Surajo Dauda bashin kuɗi Naira 165,000, inda kuma ya yi ƙararsa a caji ofis ɗin ƴan sanda domin ya biya shi kuɗinsa.

Akan hanyarsu ta zuwa caji ofis ɗin ƴan sandan ne saboda tsananin baƙin ciki da takaici ya sanya Surajo Dauda ya haɗiyi zuciya, inda ya ce ga garinku nan.

Faruwar wannan al’mari ke da wuta ya sanya ƴan uwan mamacin suka garzaya kotu domin bin haƙƙin ran ɗan uwansu a hannun wanda yake bin bashi.

Jami’an ‘yan sandane suka gurfanar da shi a gaban kotun majestire mai lamba 8 dake Gyadi-Gyadi, karkashin mai shari’a Ibrahim Khalil.

An gurfanar da Mustapha ne bisa zargin zama silar mutuwar Surajo, sai dai bayan da alƙali ya nazarci ƙarar ya bayar da belin wanda ake zargi.

A cewar lauyan wanda ake ƙara Shazali Muhammad Dahiru, kotun na da hurumin sauraron karar tare da neman belin wanda yake karewa.

Sai dai ya ce wanda yake karewa zai cigaba da zuwa kotu har zuwa sanda za a kammala shari’ar.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Ƴan Bindiga sun yi awon gaba da wasu tarin jama’a a lokacin da su ke sallar Tuhajjud a Katsina

Wasu rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa kimanin mutane arba’in da su ka haɗa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *