Zaɓen shekarar 2023: Wallahi, Buhari ba zai taɓa goyon Bola Tinubu ba – Sule Lamido

175

Tsohon Gwamnan Jigawa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Sule Lamido, ya ci layar cewa shugaba Muhammad Buhari ba zai taɓa goyon bayan burin jagaban jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu na zama shugaban ƙasa ba.

Sule Lamido ya bayyana haka ne a gurin ƙaddamar da kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP, da ya gudana a babban birnin jihar Jigawa wato Dutse. Inda ya ce shugaba Buhari ba zai iya rama bikin da dattawan yankin kudu maso yammacin kasar nan su ka yi masa a lokacin da ya ke neman shugabancin Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar ta Jigawa ya ce jam’iyyar APC mallakin mutum biyu ce wato Buhari da Tinubu.

Jam’iyyar APC mai mulki mallakin Buhari ce da Tinubu, kuma ina son in gaya muku ce Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!, shugaba Buhari ba zai taɓa goyon Bola Tinubu ba a zaɓe mai zuwa”

Sule Lamido ya ce shugaba Buhari ya cimma burinsa na zama shugaban ƙasa zango biyu amma ba tare ya cimma komai ba a manyan ƙudurorinsa guda uku da su ka haɗa magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

Haka kuma Sule Lamido ya ce Shugaba Buhari ya yaudari ƴan Najeriya tamkar yadda tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yiwa al’ummar Amurka, domin kuwa a mulkin Buhari da jam’iyyar APC akwai da yawan ƴan Najeriya da su ka shiga ruɗani sakamakon salon mulkin da su zo da shi.

Hakazalika Sule ya ƙalubalanci mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osibanjo akan ya fito nuna musu ƴan jihar Jigawa da gwamnatin APC ta tsamo daga cikin masifar talauci.

Ina ƙalubalantar mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osibanjo akan furucin da ya yi na cewa za su tsamar da mutum miliyan ashirin daga talauci. A saboda haka muna son ya nuna mana ƴan jihar Jigawa da aka tsamo su daga zafin talauci” In ji Sule Lamido

Sule Lamido dai na cikin manyan ƴan siyasar Najeriya da suka shiga zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP a kakar zaɓen shekarar 2019.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan