An Yanke Wutar Gidan Tsohon Shugaban Najeriya, Shagari Saboda Tarin Bashi

160

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna, KAEDCO, ya yanke wutar gidan tsohon Shugaban Najeriya a Jamhoriya ta Biyu, marigayi Shehu Shagari, sakamakon bashin naira N6000,000 da yake bin gidan.

A ranar 28 ga Disamba, 2018 ne tsohon shugaban ya rasu yana da shekara 93.

Kakakin Kamfanin, Abdulaziz Abdullahi ya ce tun bayan rasuwar marigayi Shagari, ba a biya kuɗin wutar gidan ba.

Abdulaziz ya kuma shaida wa jaridar cewa an ba su wa’adi ko ɗaga musu ƙafa domin biyan kuɗaɗen da ake bin su kafin a yanke wutar.

“Kamfanin ya ba su isasshiyar sanarwa don su biya kuɗin kafin a yanke wutar”, in ji Abdulaziz.

Wata majiya a gidan marigayin ta shaida wa Daily Star, wata jaridar Intanet dake Sakkwato cewa kafin mutuwar Shehu Shagari, gwamnatin jihar ce take ɗaukar nauyin kuɗin wutar tsohon shugaban.

“Kwanaki kaɗan da suka wuce, jami’an KAEDCO sun kawo bil, wanda suka ce ko mu biya ko su yanke mana wuta.

“Muka faɗa musu cewa a bisa al’ada, gwamnatin jiha ce take biyan kuɗin wutar, ba mu ba, amma suka ce wannan bai shafe su ba”, in ji majiyar.

Wani jami’in gwamnatin jihar Sakkwato da ya tattauna da Daily Star, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce rashin adalci ne a zargi gwamnatin jihar da rashin biyan kudin wutar, yana mai cewa gwamnatin tarayya ya kamata a zarga.

“Ka san kula da jin daɗin iyalan tsohon shugaban yana kan gwamnatin tarayya ne kacokan, idan gwamnatin jiha ta tallafa, ta yi haka ne kawai don tausayawa da kuma girmamawa ga tsohon shugaban ƙasar”, in ji majiyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan