Buhari Zai Ɗauki Tsaffin Ma’aikatan N-Power Aiki Na Dindindin

412

Waɗanda suka kammala shirin N-Power za su iya samun damar ayyuka na dindindin ko damar koyon sana’o’i.

Wannan dama ta yi daidai da shirin sallamar tsaffin ma’aikatan N-Power mai suna N-Power Exit da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tanada.

A ƙarƙashin wannan shiri na samar da ayyuka na dindindin, za a ɗauki wasu tsaffin ma’aikatan N-Power har su 200,000 a matsayin ma’aikatan kuɗi a wani shiri mai suna Shared Agent Network Expansion Facility, SANEF, wanda Babban Bankin Najeriya, CBN yake kula da shi.

Dama tuni an ɗauki wasu mutum 30,000 a matsayin ma’aikatan kula da ƙasa da kuma ɗaukar bayyanan jama’a a Shirin Farfaɗo Da Aikin Gona, mai suna Economic Sustainability Plan’s Mass Agric Programme, wasu da dama kuma za su amfana da wani shiri mai suna GEEP.

Wasu tsaffin ma’aikatan N-Power sun tabbatar a yayin wata tattaunawa da aka yi da su ta waya cewa an buɗe wani shafi a Intanet mai suna N-exit portal, don a tara bayanan tsaffin ma’aikatan kamar yadda shirin sallamar ya tanada.

Orioye Gbayisemore, wani tsohon ma’aikacin N-Power daga jihar Ondo ya tabbatar da cewa da yawa daga cikin abokan aikinsa sun ɗora bayansu a shafin na N-exit portal.

Haka kuma, Vivian Nkiruka Nellys, wata tsohuwar ma’aikaciya a Birnin Tarayya, Abuja, ta ce ta ɗora bayananta a ƙarshen Disamba, 2020 don cin moriyar shirin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan