Home / Lafiya / Gobara Ta Tashi A Kamfanin Haɗa Riga-Kafin COVID-19 A Indiya

Gobara Ta Tashi A Kamfanin Haɗa Riga-Kafin COVID-19 A Indiya

A ranar Alhamis ne wata mummunar gobara ta tashi a harabar Serum Institute of India, SII, kamfanin dake haɗa riga-kafin COVID-19 dake birnin Pune a Indiya.

Wutar ta fara ci ne da rana a yankin Manjari dake harabar SII, a cewar babban jami’in kashe gobara na birnin Pune, Prashant Ranpise, yana mai ƙarawa da cewa an tura jami’an kashe gobara 15 zuwa kamfanin.

Mista Ranpise ya ce kawo yanzu an iya ceto mutum uku daga cikin kamfanin.

“Tawagarmu jami’anmu tana dubawa ko akwai wasu mutane da suka maƙale.

“Ba mu san me ya haifar da gobarar ba, ko irin ɓarnar da ta yi”, ya ƙara da haka.

Sai dai gidan talabijin na NDTV ya rawaito cewa majiyoyin SII sun ce gobarar ba ta shafi ginin kamfanin da yake samar da Covishield ba, riga-kafin COVID-19 wadda Hukumar Kula da Ƙwayoyi ta Indiya ta bada izinin samarwa cikin gaggawa.

Serum Institute yana ɗaya daga cikin manya-manyan kamfanoni masu samar da riga-kafi a duniya.

A cewar Shugaban Kamfanin, Adar Poonawalla, SII yana shirin samar da riga-kafin COVID-19 har biliyan ɗaya a shekara mai zuwa.

About Hassan Hamza

Check Also

Yin ƙarin gashin idanu hatsari ne ga lafiyar ido

Animashaun ta ce gashin ido na asali yana kare idanu daga tarkace, ƙura da ƙananan ƙwayoyin cuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *