COVID-19: Ko jama’ar Kano su zauna a gida ko kuma mu sake garƙame gari – Gwamantin Kano

365

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta sa ke sanya dokar zaman gida a faɗin jihar muddin al’umma suka cigaba da bijirewa dokokin kariya na cutar Korona.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi gargadin a lokacin da kungiyoyin ma’aikatan sufuri na ƙasa reshen jihar Kanoz su ka ziyarce shi a ofis a jiya Alhamis.

Nasiru Gawuna ya ce kamata ya yi a dinga tare waɗanda ke tafiya akan titi tare da tambayarsu takunkumin rufe hanci da baki domin kaucewa sake garƙame al’umma a cikin gidajen su.

“ A baya da aka garƙame mutane ba aji dadiba, yin hakan a yanzu ka iya jefa al’umma cikin wani hali.

“Amma idan mutane suka yi watsi da matakan kariya to hakan ka iya sawa a sake sanya dokar zaman gida,” In ji Nasiru Gawuna

Mataimakin gwamnan ya ce adadin masu ɗauke da cutar ta Korona da aka samu a cikin makwanni biyu da suka gabata ya zarce adadin da aka samu a watannin zagayen farko na cutar.

Ko a jiya ma sai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana wasu tsare-tsaren soma yi wa duk mutumin da zai shiga jihar gwajin cutar korona.

Gwmanan ya shaida hakan ne lokacin da yake ƙarban bayanai daga kwamitin da ke yaƙi da annobar a Jihar, ya kuma kara da cewa zai yi aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an bi dokoki kare kai daga kamuwa da cutar a jihar,

Hakazalika Ganduje ya ce za su yi aiki tare da sarakuna da malaman addini da na jami’o’i da makarantu domin aike saƙonni bin dokokin kariya.

Daga watan Disamba shekarar da ta gabata zuwa 19 ga watan Janairu 2021, annobar ta kashe mutane 17 a Kano, mutum 72 kuma tun bullarta a ranar 11 ga watan Afrilun 2020.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan