Dalilan da ke sanyawa a haifi ‘Jariri’ da shanyeyyen hannu

  127

  Daga cikin matsalolin da jarirai kan fuskanta yayin haihuwa da kan sanya a haife su da shanyeyyen hannu akwai larurar nan da ake cewa “Obstetric Erb’s Palsy” a turancin likita. Wannan matsala tana faruwa ne sakamakon raunata turken sama (wanda ya ƙunshi tushen jijiyoyin laka ta biyar da ta shida) na dandazon jijiyoyin laka da suka fito daga wuya sannan suka sauko daga wuyan zuwa hannu domin kai saƙonnin ƙwaƙwalwa.

  Haɗarin raunata waɗannan jijiyoyi yayin haihuwa na da alaƙa da:

  1) Tankarewar kan jariri ko kafaɗa yayin haihuwa; wannan zai sa a ɗame jijiyoyin tsakanin wuya da kafaɗa.

  2) Rashin ƙwarewar ungozoma wajen janyo kan jariri yayin temaka wa mai haihuwa.

  Gwargwadon girman raunin da akai wa jijiyar; gwargwadon girman naƙasun da hannu zai samu.

  Saboda haka jijiyar za ta iya samun rauni ta hanyar:

  a) Ɗamewa

  b) Yagewa

  c) Tsinkewa ko cisgewar daga jikin laka.

  Alamomin wannan larura:

  Kamar yadda aka sani duk lafiyayyen jariri kan kasance cikin mommotsa ƙafafu da hannaye a kowanne lokaci, sai dai duk jariri mai wannan larura zai kasa iya lanƙwasa ko ɗaga hannu kamar yadda yake yi da ɗaya hannun. Wannan matsala za ta iya kasancewa a hannun hagu ko dama, wani lokacin ma duka hannaye biyun.

  Ɓarin da yake da wannan matsala zai kasance:

  1) Hannu a ɗamfare da jiki.

  2) Hannu ya murɗe/ juye ciki.

  3) Gwiwar hannu a miƙe.

  4) Yatsun hannun a dunƙule.

  Ga duk jijiyar da ta ɗame ko ta yage aikinta na kaiwa da komowar saƙonni zuwa tsokokin hannu zai gamu da cikas. Amma yayin da jijiyar ta tsinke to aikinta zai yanke ne gaba ɗaya, kuma har ta kan kai ga buƙatar yin tiyata domin haɗa ko sadar da tsokokin hannu da waɗansu jijiyoyin. Sai dai tsawon lokaci wannan hanya ta yin tiyata domin ɗinke jijiyar da ta cisge zuwa tushe ko laka kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu.

  A dukkan yanayi biyun likitocin fisiyo ne ke da alhakin farfaɗo da ayyukan jijiyoyi da tsokokin da suka sami waɗannan matsaloli.

  A tuntuɓi likitocin fisiyo da zarar an lura da jariri ba ya iya amfani da ɗaya daga cikin hannayensa yadda ya kamata bayan haihuwa.

  Physio Hausa

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan