Team Tambuwal: Ko Kawu Sumaila ya koma jam’iyyar PDP?

347

Fitaccen mai amfani da shafukan sadarwa na zamani, musamman shafin Facebook, Yasir Ramadan Gwale ya wallafa hotunan wasu fitattun mutane da su ka yi amanna da tafiyar gwaman jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ciki har da hoton tsohon mataimakin shugaban marassa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya, kuma jigo a jam’iyyar APC Honarabul Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, a matsayin mamba na wannan tafiya mai taken “Team Tambuwal 2023″

Kawu Sumaila A Matsayin Mamba A Tafiyar Aminu Tambuwal

Tuntuni dai akwai tsohuwar dangantaka da Kawu Sumaila da kuma gwamna Aminu Waziri Tambuwal, duk da cewa gwamna Tambuwal ɗin jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP.

Aminu Waziri Tambuwal A Matsayin Uban Ƙungiya

Hakazalika tun bayan zaɓen fidda gwani da aka yi na ɗan majalisar dattawa na shiyyar Kudancin Kano, inda aka fafata tsakanin Kawu Sumaila da Sanata Kabiru Gaya, inda Sanata Kabiru Gaya ya yi nasara akan Kawun, ake jin muryar Kawun yana sukar wasu daga cikin manufofin jam’iyyar APC musamman a matakin tarayya, idan yana tattaunawa da manema labarai.

Idan za a iya tunawa dai gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi takarar neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, inda ya gaza kai bantensa a zaɓen fidda gwani da aka yi a birnin Fatakwal.

A lokacin haɗa wannan rahoton wakilin Labarai24, ya tuntuɓi Honarabul Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, akan ko me za ce a game da kasancewarsa Mamba a tafiyar “Team Tambuwal” sai dai bai same shi ba.

Haka kuma kawo yanzu babu wata sanarwar ficewar Kawun daga jam’iyyar sa ta APC.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan