Siyasa: Shugaba Buhari ya sabunta rijistar sa a jam’iyyar APC

147

A yau Asabar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sabunta rijistar sa ta jam’iyar APC a mahaifarsa wato ƙaramar hukumar Daura da ke jihar Katsina.

Shugaban jam’iyar APC na riƙo kuma Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ne ya jagoranci bikin sabunta rijistar bisa dafawar sauran shugabannin jam’iyar na riƙo a matakin ƙasa.

A lokacin sabunta rijistar shugaba Buhari yana tare da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da sauran takwarorin sa gwamnoni da suka hada da na, jihar Kebbi, da Gombe, da Niger, da Jigawa, da Plateau, da kuma gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Tuni dai aka fara aikin sabunta rijistar jami’ar APC a fadin kasa baki daya, inda kowanne ɗan jam’iyyar ake bukatar ya sabunta ta sa domin bawa sababbin yan jam’iyar damar mallakar katin zama dan jam’iyar, sannan kuma a kakkabe rijistar domin fidda sunayen wadanda suka mutu ko kuma suka yi riddar siyasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan