Bitcoin: Tarihinsa, Amfaninsa, Matsalolinsa da Hukuncinsa A Addinin Musulunci (II)

  111

  7- Wannan ya kawomu ga yadda za a kalli mu’amalla da Bitcon a Musulunce. Akwai abubuwa da yawa da za a dubawa daki-daki don a fitar da hukunci da ya dace da yadda ake gudanar da Bitcoin a hain yanzu. Abin da malamai suka tsaya suna ta kokarin tantancewa shi ne dabi’ar wadannan kwaldalar ta Bitcoin shin ‘kudi’ ce ko kuwa ‘kadara’ ce? An sami wadanda suke kallon da fahimtar Bitcoin da daya daga cikin wadannan hanayoyi. A kan haka kuma suka fitar da hukuncinsu game da shi, wasu suka halatta, wasu suka haramta.-(The Shari’ah Factor in Cryptocurrencies and Tokens na Shari’ah Review Bureau a Kasar Bahrain; Shari’ah Analysis of Bitcoin, Cryptocurrency and Blockchain na Mufti Muhammad Abu-Bakar). Amma a gaskiya in an dubeta da kyau za a ga bata fada cikin ma’anar wani daga dayan abubuwan nan guda biyu ba. Haka nan yanayinta bai dace da yanayin kowane daya daga cikinsu ba.
  i-Duk da cewa masu harkar Bitcoin suna amfani kalmomin da suke nuna kudi ne kamar ‘coin’ ko ‘currency’ ko “عُمْلَة” da sauransu, amma a hakika ba kudi ba ne. Domin bai cika wasu daga cikin ka’idojin da Musulunci yake la’akari dasu a matsayin kudi ba. Wadannan sun hada da:
  a-Sai gwamnati mai ci ta amince da wannan abu a matsayin kudi wanda duk mutane zasu rika mu’amalla da shi. Malaman Musulunci sun bayyana haka a fili. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa, “Ba wanda zai buga kudi sai gidan buga kudi (na gwamnati) da izinin shugaban. Saboda mutane in ka yi musu rangwame a kansa, sai su wuce gona da iri”. Sai Imamu Abu Ya’ala ya ce, “Imamu Ahmad ya hana a buga kudi ba tare da izinin shugaban ba saboda yin hakan wani ta’addanci ne gareshi”.—(Ahkamus Suldaniyyah na Abu Ya’ala: 181; Mukaddimatu Ibnu Khaldun: sh/226; Annukud Wal-Bunuk Fin Nizamil Islami na Dr. Auf Muammad Al-Kafrawi:sh/20-56)
  قال الإمام أحمد:”لا يصلح ضرب الدراهم إلا في دار الضرب بإذن السلطان، لأن الناس إن رخص لهم ركبوا العظائم”. فعلق الإمام أبو يعلى الحنبلي قائلا:”منع من الضرب بغير إذن سلطان لما فيه من الافتيات عليه”.
  Imamu Nawawi shi ma ya yi bayanin cewa duk malaman Mazahabin Shafi’iyya ba su yada da wani ko wasu gungun mutane su ware su buga kudi ko su kirkiro wasu kudade daban ba wanda gwamnati ta yarda da shi ba. Ya ce, “Ana kin wanda ba shugaban ba ya buda kudi (kamr dinare da azurfa) ko da kuwa masu kyau ne sosai. Saboda buga kudade aikin shugaban ne. Sannan kuma ba za a aminci don za a iya samun algus da barna”.(Al-Majmu’u na Nawawi:6/11; Raudatud Dalibina na Nawawi:2/258)
  قال الإمام النوي-رحمه الله-:”يكره لغير الإمام ضرب الدراهم والدنانير، وإن كانت خالصة. لأنه من شأن الإمام. ولأنه لا يؤمن فيه الغش والفساد”.
  Wannan yana nuna cewa kamar yadda ba a son fito-na-fito da gwamnati a sha’anin mulki da gudanarwa, to haka nan ba a son a Musulunce keta alfarmar gwamnati wajen buga kudade ba tare da wani izini ba. Domin tsayuwa da daidaituwar kudi wata alama ce ta tabbatuwar gwamnati. Ibnu Khaldun ya yi bayanin cewa abubuwa guda biyu su ne ginshikan duk wata daula. Su ne karfi da kudi. Idan zata ruguje tana rugujewa ne da rygujewar wadannan wadannan abubuwa.-(Al-Mukaddimah na Ibnu Khldun: sh/294)
  A nan Nigeriya, dokokin Kasa sun hana amfani da Bitcoin da hulda da shi. A 17 na Janairu na 2017 Babban Banki Kasa (CBN) ya haramta amfani da shi ta kowace fuska. Ma;anar wannan da a ce za asami wani yake wani kar da sunan ya rike masa kudi ta hanyar Bitcoin, ba za a saurari karar ba. Saboda ba ta sabawa dokin kasa.
  Sai dai yana da kyau a sani cewa, a zamani irin wannan ba wai yarda ko rashin yardar wata kasa kadai shi ne abin la’akari wajen halatta wani abu ko haramtashi ba. Saboda a yanzu kasashe sun yarda da tsarin banki mai ruwa, amma wannan bai sa an ce shi kenan yin hakan ya halatta ba. A lokacin da Daular Musulunci take da karfi da iko, ana gudanar da abubuwa a kan Shariar Allah, a lokacin ana iya cewa ba laifi ana iya laakari da wasu abubuwan saboda gwamnati ta yarda shi. Amma ko a da can har da kuma yanzu, ana duba yadda abu yake cikinsa-da-bayansa, sannan sai malamai su bada fatawa da zata bayyana matsayinsa a Shari’a na halasci ko haramci. Wannan wani abin dubawa ne da kyau.
  b-Bayan gwamnati ta yarda da duk abin da take ganin za iya tsayawa a matsayin kudi, za a ga duk mutane sun yarda da su a mu’amalolinsu na yau-da-gobe. Wannan shi ne abin da Imamu Malik yana cewa, “Da a ce mutane zasu yarda da fatun dabbobi a tsakaninsu a bugasu a matsayin kudade, da ba zan so a sami jinkiri ba idan sun yi canja fata da dinare da azurfa”.-(Al-Mudawwanah: 3/5. A dada duba ra’ayin Hanafiyya a Littafin Tanbihur Rukud Ala Ahkamiln Nukud na Ibnu Ibidn: sh/25)
  قال الإمام مالك:”ولو أن الناس أجازوا بينهم الجلود حتى تكون لها سكة وعين، لكرهتها أن تباع بالذهب والورق نظرة”.
  Ma’anar maganarsa ita ce duk abin da mutane suka hadu a kan cewa kudi ne, kuma suka gina rayuwarsu a kansa, ya zama kudi. Duk hukunce-hukuncen Shari’a na kudi zasu shafeshi. Kudi suna da sifar zamowa tsanin da kowa-da-kowa zai yi amfani da shi wajen saye-da –sayarwa. Ba a la’akari da kudaden da suka zamo masu gudanawa tsakanin wasu tsurarun mutane.-(Al-Warkun Nakadi na Sheikh Abdullah bn Mani’i sh/17). Bitcoin ba kudi ba ne da kowa-da-kowa yake da ikon amfani da su cikin sauki ba. Kudade ne-in har an yarda ma cewa kudin ne-da suke yawa a kan internet kurum. Wadanda suke huldar su kadai suka san da su, kunzumin mutane ba su da alaka da wadannan kudaden na boye!
  c- Kudi abu ne na zahiri da yake zamowa ma’aunin kimar abubuwa a fadin duniya, ta yadda abin da aka saya ya zamo daidai da kimar kudin da a ka sayeshi da su.-(Al-Mugni na Ibnu Kudama:5/419). Don haka ne ake da kudi kala biyu:
  Na daya: Abubuwan da su da kansu kudade ne kamar gwal da azurfa. Har yanzu ana daukar gwal cikin manyan abubuwan da kasashe suke ajiyewa a matsayin (Foreign Exchange Reserve).
  Na biyu: Abubuwan da gwamnati ta yarda da su a matsayin kudade kamar takardun kudi na Naira, Riyal, Dollar, Euro da sauransu. Tuntuni Malamai suka tabbatar da karbar takardun kudi. Kafin wannan zamanin ma Imamu Malik ya fadi maganar da aka kawo a sama. Har ila yau kuma Shehul Islam Ibnu Taimiyyah shi ma ya yi bayanin da za a dora takardun kudi a kansa. Ya ce, “Dinare da azurfa ba su da wata wani iyaka ta al’ada ko ta Shari’a. Makomar lamarinsu bata wuce al’ada da abin da mutane suka yarda da shi a tsakaninsu. Saboda su kudi tun asali ba manufarsu kenan ba. Manufar it ace su zamo ma’auni na abubuwan da ake mu’amalla da su kurum. Dinare da Dirhami ba su da kansu ne manufa ba. A na daukarsu ne a matsayin tsani kurum don a yi mu’amalla da su. Don haka ne ma suka zamo kudade, sabanin sauran dukiya, wadanda asalin manufar samuwarsu ita ce a yi amfani da su”-(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyyah: 19/251)
  قال شيخ الإسلام ابن تيمية-رحمه الله-:”وأما الدرهم والدينار فما يعرف له حد طبعي ولا شرعي. بل مرجعه إلى العادة والاصطلاح. وذلك لأنه في الأصل لا يتعلق المقصود به. بل الغرض أن يكون معيارا لما يتعاملون به. والدراهم والدنانير لا تقصد لنفسها، بل هي وسيلة إلى التعامل بها. ولهذا كانت أثمانا؛ بخلاف سائر الأموال. فإن المقصود الانتفاع بها نفسها. فلهذا كانت مقدرة بالأمور الطبعية أو الشرعية”.
  Manufar kawo wannan don a nuna cewa Bitcoin bai sami irin wannan darajar ta karbuwa a matsayin kudi ba a kasashe da yawa ba. Abin da yake faruwa dangane da shi shi ne wani mutum ko wasu mutane ne kurum suka kirkireshi a kan internet, sannan tsakanin duhun-dare da sanyin-safiya suka bace aka kasa ma gano ko waye har yanzu!
  d-Sannan kuma ana biyan kudade idan wani ya salwantar da su. Ita kuwa kwandalar Bitcoin, in ta salwanta, ba mai biya ko ya dawo da ita. Don haka ciniki da hulda da ita ya shiga haramci saboda garari da hadarin da yake ciki.

  e-Bitcoin ya fi kama da kudin-ganye (Alfulus): Ana kirkirar kudin ganye ne saboda dalilai da yawa, musamman don a shirgar da su cikin mutane su bada mai kyau a basu mara kyau. Ibnul Kayyim ya yi bayani mai gamsarwa a kan yanayin kudin-ganye. Idan aka yi la’akari da bayaninsa a kan Bitcoin za a ga kamannin ya bayyana sosai. Ya ce, “Kamar yadda ka gani dangane da rugujewar mu’amallar mutane da irin cutuwa da tale samunsu idan suka fara amfani da kudin-ganye (Alfulus) a matsayin kadara don samun riba. Yin haka sai ya kawao cutuwa da zata game ko’ina, zalunci ya yadu. Da an daukesu a matsayin kudi na-bai-daya, baya karuwa ko ya ragu, wanda zai zamo ma’unin abubuwa, amma ba a auna shi da kadarori, da an yi haka da lamarin mutane ya gyaru…Saboda ba a burin samun kudi su a karan-kansu, sai dai ana bukatarsu ne don akai ga sayan kadara/haja. Idan kudade su da kansu suka zamo kadara, ana hankoron a samesu kamar kadara, sai lamarin mutane ya lalace. Wannan bayani ne na hankali da ya shafi zallan kudi, ba zai tsallaka zuwa wasu Abubuwan ba”.-(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/156-157).
  قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-:”كما رأيت من فساد معاملاتهم، والضرر اللاحق بهم، حين اتُّخذَت الفلوس سلعة تعد للربح، فعم الضرر، وحصل الظلم. ولو جعلت ثمنا واحدا لا يزداد ولا ينقص بل تُقوّم به الأشياء، ولا تقوم هي بغيرها لصلح أمر الناس…فالأثمان لا تقصد لأعيانها، بل يقصد التوصل بها إلى السلع. فإذا صارت في أنفسها سلعا تقصد لأعيانها، فسد أمر الناس. وهذا معنى معقول، يختص بالنقود لا يتعدى إلى سائر الموزونات”.
  Malamai irinssu Imamu Gazali suna fada cewa, “Idan kudin-ganye suka sami karbuwa kamar kyawawan kudade, to sai su zamo kamar kadara, a maganar malamai mafi inganci”- (Nuzhatun Nufusi Fi Bayani Hukumit Ta’amuli Bil Fulusi na Ibul Ha’imi Ahamd bn Muhammad, sh/47)

  ii-Duk da cewa Bitcoin ya so ya yi kama da ‘kadara/haja’ (Legit commodity/goods) amma ba kadarar ba ce. Domin ita kadara/haja tana zamowa a hannu sannan ta biyawa wanda yake da ita wata bukata ta musamman kamar ya sa a cikinsa ko ci ko ya sha ko ya shiga in gida ne ko ya hau kamar mota ko keke da doki da sauransu. Haka nan kadara tana samun kula ta wajen tabbatar da kyau da tsari daga hukumomi. Bitcoin kuwa bata da irin wadannan sifofi. Saboda Bitcoin tna gujewa hukumomi. Sannan kuma iyakacinta kan internet ba kari. Shi ya sa bai dace ba a dauketa a matsayin kadara har kuma a gina hukunci na halaccin tsarin bakidaya a kan haka.
  iii- Bitcoin ba shi da zibi da tsari irin na katinan da ake ajiye kudade a cikinsu kamar su Visa Card, Master Card da sauransu. Saboda su wadannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulda da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane!
  8-Bisa irin bayanai da aka kawo a karkashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a karkashin lamba ta 7, duka wadannan suna nuna cewa wannan harka ta Bitcoin tana kunshe da abubuwa da yawa da suka isa a ce ‘Haram’ ce bisa dokokin Shari’a. Ga bayanin dailan haramcin a dunkule:
  i-Riba: Riba tana shiga hadahadar Bitcoin musaman ta fuskoki biyu:
  Fuska ta daya ana sayar da kwandalar bitcoin da bitcoin da fifiko da karin wata a kan wata, wanda yake riba ne. Sannan a wasu lokutan ana samun jinkiri, ba a samun hannu-da-hannu ko da ‘bayarwa ta ma’ana’ ce a wajen canji da ake yi tare da sauran kudade.
  Fuska ta biyu kuma, kamfanonin da suke saye da sayar da Bitcoin a kasuwannin kudi, wato (brokers), suna karbar kudin mutan kamar N 5,000, sai su ranta masa wasu kudaden masu yawa kamar N 50,000 a kan wadancan. Daga nan sai su zubasu a sayen ‘share’. Idan kudi suka habaka, aka ci riba, sai su bawa mutum iya kason da ya dace da kudinsa, su kuma su rike ragowar a matsayin (commission). Wannan shi ake kira da ‘Leverage’, wanda yake haramun ne ta fuskoki da yawa. Daga ciki dai Akwai bashi da riba da aka yi da sunan wanda ya sa kudi tun farko. Sannan kuma ya yarda da ya taimaka a ci riba. Wannan duka haram ne.
  Idan kuma an fadi, to duk kudin mutum (N 5,000) din baki daya sun salwanta, ya yi asararsu! Wannan bangaren ya shiga tsarin caca zindim!
  ii- An gina Manhajar Bitcoin a kan tsarin caca. Shi ma wannan zai iya zamowa ta fuskoki da yawa, musamman gida biyu.
  Fusaka ta daya ita ce wadda ta gabata a misalin da aka fada a lamabar sama cewa idan mutum ya sa kudi misali (N 5,000), shi kuma ‘broker’ ya kara, sai a ka sami asara, to kudin mutum sun nutse baki daya, ba zai sami komai ba.
  Fuska ta biyu kuma kamfanomin da suke fafutukar samo ‘coin’ din ta hanyar ‘mining’ suna kashe dimbin kudade su zunduma cikin zabari tare da sauran masu nema, a karshe sai guda daya ne zai iya samu a cikin minti goma. Sauran ba wanda zai sami wani abu. Kowane irin abu suka kashe na dukiya ya tafi a banza.

  iii-Cin dukiyar mutane ba-gaira-ba-dalili: Kula da dukiyoyin mutane da kiyayesu daga salwanta yana daga cikin manufofin Shari’a. Akwai sauki sosai ta hanyar Bitcoin a sami damar cin dukiyar mutane ba tare da wata wahala ba. Saboda yadda farashin Bitcoin yake gwauran tashi a dan kankanin lokaci, yana huwacewa wasu su azurta da kudaden mutane ba gaira-ba-dalil. Sannan kuma ya sauka adan lokaci, ta yadda wasu zasu yi gagarumar asara. Wannan yana bada tsoro har ana tunanin cewa akwai wasu a boye masu ci da gumin sauran mutane! Tsarin hawa da saukar Bitcoin ya wuce tsarin yadda aka san cinikayyar canji a kasuwar duniya ta yadda hawa da saukar ba wani mai yawa ba ne, amma ba ya ninninka ba. Misali Bitcoin ya taba ninkawa har sau dari uku a 2017 sannan kuma ya ruguzo! Wannan yana nuna Bitcoin ba kudi ba ne da za a dogara da shi. Wasu daga cikin msana tattalin arziki suna cewa, ‘hauhawar Bitcoin kamar tashin kumfa take’ (bubble), nan da nan zata sauka a dawo kasa!
  Imamu Ibnu Kayyim ya fayyace wasu ka’idoji da za a fahimci yadda tsarin kudi yake a Musulunci. Ya ce, “Dirhami da Dinare kudade ne na kadarori da kayan sayarwa. Abin da ake nufi da kudi shi ne ya zamo ma’auni, wanda za a rika kimanta kimar sauran dukiya da shi. Don haka ne dole ya zamo mai iyaka, aka san gwargwadon yadda zai kai ya kawo, ba ya tashi samai sosai, ko ya fadi kasa warwas! Domin idan kudi yana tashi , yana sauka kamar wata kadara, ba zai zamo man kudi da za a rika la’akari da shi wajen kimar kayan sayarwa ba. Sai duk su zamo kadara ne, tare da cewa bukatar mutane zuwa ga tsuran kudi wanda za su rika la’akari da shi dangane da kayan sayarwa, wannan bukata ce ta larura, da ta shafi kowa. Shi kuwa tabbatar da wannan sai da wani farashi da za a san kimar abubuwa da shi. Shi ma wannan sai da wani tsarin kudi da za rika yiwa abubuwa kima ta kima da shi, wanda zai zarce a kan hali daya, ba wai shi ya zamo ana yi masa kima da wani abin ba, saboda ya zamo kadara da zai tashi ya sauka. Yin haka kuwa zai bata tsarin mu’ammalar mutane, sabani ya shiga tsakaninsu, cutuwa ta tsananta a cikinsu” -(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/157)
  قال الإمام ابن القيم-رحمه الله-“فإن الدراهم والدنانير أثمان المبيعات. والثمن هو المعيار الذي به يعرف تقويم الأموال، فيجب أن يكون محدودا مضبوطا لا يرتفع ولا ينخفض. إذ لو كان الثمن يرتفع وينخفض كالسلع لم يكن لنا ثمن نعتبر به المبيعات، بل الجميع سلع. وحاجة الناس إلى ثمن يعتبرون به المبيعات حاجة ضرورية عامة. وذلك لا يمكن إلا بسعر تعرف به القيمة. وذلك لا يكون إلا بثمن تُقوّم به الأشياء، ويستمر على حالة واحدة. ولا يُقوّم هو بغيره، إذ يصير سلعة يرتفع، وينخفض، فتفسد معاملات الناس، ويقع الخلف، ويشتد الضرر”.
  Wannan bayani ne mai matukar karfi, tare da cewa Ibnul Kayyim ya yi shi ne bisa duba da la’akari da tsarin kudi tuntuni. Sai dai a zahiri bayani ne kamar yau aka yi shi da ya shafi irin gararin da Bitcoin yake son jefa mutane a ciki. Domin a halin yanzu mu’amallar da ake yi da Bitcoin din tare da cewa na yi masa kirarin cewa kudi ne, amma mu’amallar irin wadda Ibnul Kayyim ya fada tana so ta mayar da shi kamar kadara/haja ba kudi ba !!
  iv-Garari: Akwai garari a ciki saboda idan an tura kudade ba za a iya shan kansu ba a dawo da su ba, idan misalign an fasa cinikin. Sai dai in wancan bangaren wanda ba a san kowaye ba, ya tausaya ya dawo da su. Sannan wanda aka yi ciniki da shi zai iya cinyewa mutane kudadensu ba tare da an kaishi wurin hukuma ta hukunta shi ba. Don haka wanda yake wannan mu’amalla ya shirya karbar mummunar asara da abokan mu’amallar ba za su san mai yake ciki ba ma ballantana su yi tunanin tausaya masa ba!
  v-Jahala: A cikin huldar Bitcoin akwai rashin sanin yadda wasu abubuwan suke gudana da yawa. Domin ba komai ne a fayyace ba. Hatta wanda mutum yake haulda da su, mutum bai gama fahimtar su waye ba, ta yaya suka tara kudadensu, shin yana taimakawa marasa gaskiya ko kuwa? Da dai sauran irin wadannan tambayoyi masu wahalar amsuwa. Muhimmi dai ana so a gina ciki ba bu jahiltar abin da cikin ya kunsa. Imamu Ibnul Arabi Al-maliki yana cewa, “Malaman wannan al’umma sun hadu a kan cewa cinikayya bata kulluwa sai ga abin da aka sani, daga wanda aka sani, da abin da aka sani, ta kowace irin fuska wadda za a iya samun sanayar”-(Al-Kabas Shurhul Muwadda na Ibnul Arabi Al-Maliki:2/786-803)
  قال الإمام ابن العربي المالكي-رحمه الله-“وقد اتفقت الأمة على أنه لا يجوز إلا بيع معلوم من معلوم بمعلوم- بأي طرق العلم وقع”.
  9- Kasancewar duk ma’anoni guda uku da suke ruguza cinik wato, riba, garari da algush, sun hadu a wannan mu’amalla ta Bitcoin, ya wajaba ga wanda yake yin hadahada da Bitcoin da ya dakata, ya daina. Ya sayar da abin da ya tara a lalitarsa sannan ya kwashe uwar kudinsa, ragowar kuma ya badasu sadaka ko ya sa su a wani aikin alheri da al’umma zata amfana da su bakidaya. Wanna saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce, “In kun tuba, to sai ku rke uwar kudinku, ba ku zalinci kowa ba, kuma ba a zalinceku ba”-(Bakara2:279)
  “وَإِنْ تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَالِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُونَ”-(البقرة:279)
  10-Mu’amallar Bitcoin tana da dan rikitarwa. Abubuwa da yawa ba su bayyana ba a cikinta sai daga baya. Wannan ya sa malamai sun yi dan yi sabani wajen fitar mata da hukunci, musaman a shekara ta 2017, a lokacin da lamarin Bitcoin ya burinkasa, mutane suka fadaka da irin yadda zata kawo musu kudi suna kwance, ba wata wahala.
  Malamai a daidaikunsu da kuma Majalisu sun zauna a lokuta daba-daban don su tabbatar da hukuncin wannan mu’amalla. Daga cikin wadanda suka tattauna mas’alar, suka kuma tabbatar da cewa ta sabawa Shari’ar Musulunci akwai Majalisar Malamai ta Kasar Turkiyya (Darul Ift’it Trukiyyah, 29/11/2017: https//goo/gl/KVqoyr), da Misra (Darul Ifta’il Misriyyah, 28/12/2017: https//goo/gl/WTMpdu); da Falasdinu (Majlisul Ifta’ Al-Filisdiniyya: https//goo/gl/TEMmlu).
  Haka nan, akwai taron karawa-juna-ilimi da aka yi a Doha ta kasar Qatar (4th Doha Islamic Finance Conference) a January, 2017 M. sun tattauna irin kudaden da ake hulda da su ta hanyar internet kawai. Masu taron, wadanda suka hada da Dr. Abdussattar Abu Ghudda-Allah ya yi asa rahama- da Dr. Aliyu Kardagi da sauran masana a fagen tsarin tattalin arziki na Musulunci, sun tabbatar da cewa irin wadannan sababbin cinikayya suna da rikitarwa da hadarin gaske, musaman da yake ba wani nassi da ya zo a kansu. Amma fitar da hukunci ga irin wadannan mas’aloli ba zai gagari masana Fikihu ba a cikin malaman Musulunci.
  Bayan haka manyan malamai sun dada zama a karkashin Majma’ul Fikihil Islami Addauli (International Islamic Fiqh Academy) a farkon shekara 1441 H./2019, a inda suka tattauna sosai a kan dabi’ar wannan mu’amalla.
  11-Akwai wasu abubuwa wadanda idan Bitcoin da sauran huldodi masu kama da shi suka cikasu za a iya la’akari da su a janye harmcin da yake kansu a yanzu kamar yadda Sheikh Aliyu Kardagi ya bada shawara. Wadannan abubuwa sun hada da:
  i-Gwamnati ta dauki Bitcoin a matsayin kudi. Don haka sai sami wata kasa ta yarda da tsarin Bitcoin da makamantanta, ta yadda Babban Bankin kasar zai aminci da hulda da ita. Sai a sawa manhajar ka’idoji. Yawancin kasashen da ake cewa a yanzu sun karbi tsarin, sun karba ne a dunkule, amma ba su sa dokikin da zasu maida Manhajar ta zamo karkashin Babban Bankin wadannan kasashe ba. Don haka kada wani ya rudu da zancen ai Akwai kasashen da suka yarda da tsarin.
  ii- A dauki Bitcon a matsayin ‘kadara/haja’. Wannan kuma sai an sami kamfanonin da zasu rika juya Bicoin din a matsayin “share”, ta yadda kowace ‘share’ zata zamo a na ganinta cikin jumlar tsarin wadannan kamfanonin. A halin yanzu Bitcoin ba shi da wannan tsarin ta kowace fuska.
  iii- Ya zamo kamar tsarin su Visa Card, Credit Card, da sauransu. Ta yadda za a sami wasu kamfanoni da zasu dauki gabaran gudanar da tsare-tsarensa da hadahadarsa da shige-da-fitarsa kamar yadda ake yiwa wadancan katika.
  Yin daya daga cikin wannan zai bawa Bitcoin wata sabuwar kima ta halacci a idon Musulmi.
  A karshe, hadahadar Cryptocurrency a karan kanta ba za a iya cewa haram ba ce, ba laifi Musulmin duniya su fara tunanin yadda zasu ci moriyar hakan ta hanyar da ta halatta wadda aka nuna a nan sama kadan. Saboda da alamu nan gaba kadan duk duniya za a raja’a a kan Degital Money. Amma dai a halin yanzu idan aka yi la’akari za a ga cewa wannan mu’amalla ta Bitcoin ta fada bangarori da yawa na haramci a Shari’ah, ba wai wani bangare daya ne kurum ba.
  A karshe muna yiwa Allah godiya, da fatan ya sa mun dace.

  Farfesa Ahmad Murtala, Malami ne a sashen harkokin addinin Musulunci da Shari’a na jami’ar Bayero da ke Kano.

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan