Ya Kamata Masu Faɗa A Ji A Najeriya Su Riƙa Yaba Wa Gwamnatina— Buhari

148

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya kamata masu faɗa a ji a ƙasar su riƙa yaba wa gwamnatinsa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a mahaifarsa, Daura, a lokacin da yake sabun ta rijistarsa ta jam’iyyar APC.

Shugaban ya yi kira ga masu faɗa a jin su riƙa yin tunani da adalci tare da yaba masa bisa ayyukan da ya aiwatar a yayin da suke sharhi a kan gwamnatinsa.

“Ina so masu faɗa a ji namu su kasance masu nazari da kuma tuna cewa mun karɓi mulki ne a 2015. Su tuna halin da muke ciki a wancan lokacin, da kuma kuɗin da ake da su a lokacin da kuma ayyukan da muka taras.

“Daga shekarar 1999 zuwa 2014, ƙasarmu ta fitar da gangar man fetur 2.1m kuma ana sayar da kowace ganga a kan fiye da dala 100 a wasu lokuta. Tattalin arziƙinmu ya fi shiga mummunan hali a lokacin da muka zo, hakan ne yasa muka ceto wasu jihohi daga durƙushewa ta yadda za su iya biyan albashi da fansho. Yanzu al’amura sun fi daidaita,” in ji Shugaba Buhari, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan