Kiwon Gafiya da Ɓeraye zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya – Masani

514

Wani mashahurin masanin dabarun kiwon dabbobi mai suna Dakta Yemi Pooola, ya ce idan aka maida hankali ga kiwon burgu da gafiya za a iya bunkasa hanyoyin samun kudi sosai a Najeriya, tare kuma da samun lafiyayyen nama mai gina jiki.

Popoola wanda ma’aikaci ne a Cibiyar Bincike da Horas da Dabarun Noma ta Ibadan, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, a ranar Litinin.

Ya ce cin naman burgu da gafiya ya na kara gina jiki, domin nama ne mai rai da lafiya matuka.

“Sana’ar kiwon gafiya da burgu ba wata walaha ke gare ta ba. Domin ko a bayan gida mutum zai iya kebe wani dan wurin da zai rika kiwon abin sa. Kuma ba ta bukatar jari mai kauri. Da kudi kadan ma sai mutum ya fara, kuma ya samu riba mai yawa.

“Kiwon burgu na da matukar riba, saboda nama ne da ake matukar bukata sosai, kuma da wuri kankane sai mutum ta kiwata gafiya da yawan da zai samu gagarimar riba. Ga su kuma da saurin haihuwa da saurin girma.”

“Naman burgu ko gafiya da aka sani da suna ‘bush meat, ana bukatar sa sosai a Najeriya. Sannan kuma babu wata ka’ida ko sharadi wajen cin naman sa.

“Naman burgu da gafiya ya fi naman sa, rago, tinkiya ko akuya tsada. Kuma idan burgu ya girma, zai iya kai nauyin kilogiram 6 zuwa 7. Kai idan dankareren burgu ne ma zai iya kai nauyin kilogiram 10.

Akwai nau’in macen burgun da kan haifi ‘ya’ya biyu zuwa hudu a shekara. Sannan kuma akwai wata na nan mai kama da beran-Dinka, wadda ke haihuwa duk bayan watanni shida.

Premium Times

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan