Rashin Tsaro: Wuta Na Ci A Ƙofar Gidan Buhari Ya Kasa Kashe Ta— Obasanjo

99

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya roƙi Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da ya tashi don ganin ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, ya kuma tunkari kashe-kashen da ake ci gaba da samu a ƙasar nan.

Jaridar PUNCH ta jiyo tsohon Shugaban Najeriyar yana bayyana haka a yayin da yake jawabi a wata tattaunawa ta Intanet da Toyin Falola, wani masanin Tarihi ranar Lahadi.

Mista Obasanjo ya ce matakin da Shugaba Buhari ya ɗauka na sauya hafsoshin tsaro ba wani abin murna ba ne, yana mai ƙarawa da cewa ba zai ce komai ba bisa ƙwazonsu sai bayan wata uku ko shida.

Ya ce ya yi tunanin Shugaba Buhari zai yi ƙoƙari sosai wajen yaƙar cin hanci, amma bai san yana da halayyar alfarma ba.

“Ina jin na san Shugaban Ƙasa Buhari saboda ya yi aiki da ni. Amma nakan tambayi mutane, shin ban karanta tarihinsa ba ne sosai yadda ya sauya daga Buharin da na sani? Ban yadda da mutanen da suke cewa wani sabon Buhari muka samu daga Sudan ba da dai sauran shirme”, in ji shi.

“Na san abinda na yadda da shi shi ne iyakar abin da zai iya yi kuma na yi rubutu a kan haka— ba shi da ƙarfi a Tattalin Arziƙi, ba dukan mu ba ne muke da ƙarfi a wani abu ba, amma kana buƙatar ka samu cikakkiyar masaniya a kan sa don ka iya bada umarni. Kuma ba shi da ƙarfi sosai a harkokin ƙasashen waje, amma ina tunanin yana da ƙarfi sosai a aikin soja.

“Daga ƙwazonsa na lokacin da yake shugaban soji, na yi tunanin zai yi ƙoƙari wajen yaƙar cin hanci. Ban san Buhari yana da alfarma ba, wataƙila saboda bai fuskanci irin wannan yanayi ba a lokacin da ya yi aiki da ni.

“Da abin da na gani yanzu, na yi imani cewa wataƙila zai fara tunanin barin wata manufa. Wata ƙila zai koyi darasi daga abin da ya faru a ‘yan kwanakin nan.

“Idan kana Shugaban Rundunar Soji, kuma ana kashe-kashe a bayan gidanka, ya kamata ka farka. Shugaban Ƙasa ya sauya hafsoshin tsaronsa bayan sun shafe fiye da shekara biyar ba tare da sun yi wani abin a-zo-a gani ba, wasu mutane kuma suka fara murna.

“Ban san ko ɗaya daga cikin mutanen da aka naɗa a matsayin hafsoshin tsaro ba, amma za ku ji ta bakina daga nan zuwa wata uku ko shida saboda a cikin wannan lokaci, za mu iya nuna abin da za su iya yi”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan