Home / Kuɗi/ Tattalin Arziƙi / Tattalin Arziki: Darajar ‘Naira’ na ci gaba da faɗuwa wanwar

Tattalin Arziki: Darajar ‘Naira’ na ci gaba da faɗuwa wanwar

A yau Litinin Darajar naira ta ƙara faɗuwa kan dalar Amurka a kasuwar bayan fage. Ƴan kasuwa sun ce darajar kuɗin na yi mugunyar faɗuwa inda ake sayar da dala ɗaya kan naira 480 a kasuwar bayan fage.

Ƙarin kashi 20 fiye da farashin da Babban Bankin Najeriya ya ƙayyade kan naira 381.

Buƙatar dala na ci gaba da ƙaruwa, kuma wannan ke sanya matsin lamba a kan naira.

Masu shigo da kaya na fuskantar ƙalubale yayin da kuma masu saka jari a kasuwar canji wasu suka fice.

Ƴan kasuwa sun ce har yanzu Babban Bankin Najeriya bai ci gaba da sayar da dala ba a wannan shekarar ga masu saka jari na ƙasashen waje, kuma bai sayar da kuɗaden waje ba ka kamfanonin canji a makon da ya gabata.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Micheal Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya cika shekaru 85 da haihuwa

A yau Litinin 10 ga watan Mayun shekarar 2021 mutumin nan da ya zama tutar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *