Abdullahi Abbas bai dace ya zama shugaban kowacce irin siyasa ba – Mu’az Magaji

235

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Mu’az Magaji mai laƙabin ɗan Sarauniya ya ce sam shugaban riƙon na jam’iyyar APC Abdullahi Abbas bai cancanci ya zama shugaban kowacce irin jam’iyyar siyasa ba.

Mu’az Magaji ya bayyana hakan ne a safiyar yau Talata, a shafinsa na facebook, inda kalaman na sa su haifar da muhawara a tsakankanin masu bibiyar shafin na sa.

Sam Abdullahi Abbas, bai da ce ya zama shugaba a siyasa ba, kullum yana ƙara mana ƙiyayya ne ba soyayya ba. Maganar gaskiya ita ce lokaci yayi da ya kamata a sallame shi ya kama wani aikin can da zai ƙasaitar sa ba tare da yayi mana ɓarin tafiya ba, don mu bama masa kyashi” In ji Mu’az Magaji

Ya ƙara da cewa “Idan har mu ka yi shiru da ire-iren wannan katoɓarar, Kanawa ba za su ce da mu komai ba, amma ta ciki na ciki, sai ranar alkalanchi, 2019 darasi ce”

Ba wannan ne karon farko da Injiniya Mu’az Magaji, ke irin wannan furucin akan Abdullahi Abbas ba, domin ko a cin watan Janairu sai da Mu’azun ya ce idan ba tsoro ba shugaban riko na jami’iyyar APC Abdullahi Abbas yaje ayi masa gwajin kwaya kamar sauran ƴan takarar ƙananan hukumomi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan