Sanata Kabiru Gaya na jam’iyyar APC mai wakiltar Kano ta Kudu ya ce ya kamata Kudancin Najeriya ya fitar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a 2023.
Sanata Kabiru ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattauanawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Abuja.
Ya ce Arewacin Najeriya ya tsayar da da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa har sau biyu.
“Ina alfahari da Shugaban Ƙasa saboda na yi imani yana iya ƙoƙarinsa.
“Game da batun shugabanci a 2023, zan goyi bayan Shugaban Ƙasa daga Kudancin ƙasar nan. Na yi imani lokaci ya yi da za mu samu Shugaban Ƙasa daga Kudancin ƙasar nan, Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ya fito daga Arewa.
“Ina jin zai fi zama adalci a zagaya da shugabancin don mutane su samu ƙwarin guiwa a kan tsarin, duka Arewa da Kudu za su iya ɗaukar juna. Najeriya tana buƙatar kasancewa ƙasa ɗaya. Ƙasa ɗaya mai haɗin kai”, in ji shi.