Gwamnatin jihar Kano ta amince ta mayar wa ma’aikatan jihar albashin da ta yanke musu a watannin da suka gabata sakamakon ƙarancin Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida, wato IGR.
Gwamnatin dai ta ce annobar COVID-19 ce ta haifar mata da ƙarancin kuɗaɗen shiga, abin da yasa ta dawo biyan ma’aikatan N18,000.
Shugaban Majalisar Sasantawa ta Haɗin Gwiwa Tsakanin ‘Yan Ƙwadago da Gwamnati, JNC, na jihar Kano, Kwamared Hashim Saleh ne ya bayyana haka ranar Litinin da daddare, yana mai gode wa gwamnatin jihar Kanon bisa cika alƙawarinta.
Kwamared Hashim ya kuma yaba wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa “girmama yarjejeniyar da kuma koma wa kan mafi ƙarancin albashi (na N30,600) wanda tuni an fara aiwatarwa tun watan da ya gabata”.
Saboda haka ne sai Kwamared Hashim ya yi kira ga ma’aikatan da su saka wa gwamnatin bisa wannan abin kirki da ta yi musu ta hanyar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A baya dai, Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, da ƙungiyoyin da suke ƙarƙashinta sun yi ta tattaunawa da gwamnatin jihar Kano, suka kuma fitar da barazanar tafiya yajin aiki sakamakon yanke albashin da aka yi wa ma’aikatan a watannin Nuwamba da Disamba a bara.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta yanke wa ma’aikatan albashin ne don ta samu damar ci gaba da aiwatar da ayyuka, tana mai cewa hakan zai ya hana ta biyan wasu ma’aikata ta ƙyale wasu, zai kuma hana ta korar ma’aikata.