APC Na Shirin Tsayar Da Jonathan Takarar Shugaban Ƙasa A 2023

109

APC Na Shirin Tsayar Da Jonathan Takarar Shugaban Ƙasa A 2023
Wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa na cewa masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan rahotannin da suke cewa jam’iyyar APC mai mulki na zawarcin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan domin ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a karkashin tutar jam’iyyar a zaɓen 2023.

An ce wasu gwamononi daga Arewacin ƙasar ne ke matsa wa wajen ganin hakan ta tabbata, inda suka bayar da hujjar cewa saboda wa’adi ɗaya kawai tsohon shugaban ƙasar zai yi, sai mulki ya sake koma wa yankin Arewacin ƙasar, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

To amma masana game da siyasar ƙasar na cewa hakan alama ce da ke nuna rashin aƙida a tsakanin ‘yan siyasa masanman ‘yan jam’iyyar ta APC mai mulki, a cewar rahoton na BBC Hausa.

A cewar BBC Hausa, masanan, wasu manyan jam’iyyar sun gwammace tsohon shugaban ƙasar ya kasance magajin shugaba Buhari, saboda ba zai musu bi-ta-daƙulli ba, bayan haka ma zai fi daɗin tafiya a kan wanda zai fito daga wata shiyya ta daban, ko daga shiyyar kudu maso yammaci ko kudu maso gabashin kasar, sannan kuma ba zai wuce wa`adi daya ba,kuma bayan hakan sai mulki ya dawo ga ‘yan arewa ganin cewa tun a baya ya yi wa’adi guda.

Dr Abubakar Kari, malami ne a Jami’ar Babban Birnin Tarraya, Abuja, ya ce ”Wannan na nuna cewa a siyasar Najeriya babu aƙida babu alƙibla, kuma komi ya na iya faruwa.

A cewarsa, ”Idan kuma ba haka ba Goodluck Jonathan wanda a baya aka taru baki ɗaya aka ce ya gaza, ya kasa, mulkinsa ya yi rauni ƙwarai da gaske kuma a ce shi ne yanzu za a riƙa zawarcin sa ya dawo ya sake mulkin ƙasar.

”Irin wannan komen ba alheri ba ne ga ƙasa kamar Najeriya”, ya ƙara da haka.

Zuwa yanzu dai, babu wani bayani daga jam`iyyar APC mai mulki da aka ce ta na neman zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan don ya mata takara a zaɓe mai zuwa na 2023.

Bugu da ƙari har daga ɓangaren tsohon shugaban ƙasar babu wani da ya fito ya ɗaga yatsa domin musunta wannan maganar.

To amma ta wani ɓangare wasu ‘ya’yan jam’iyyar ta APC na cewa rungumar tsohon shugaban kasar babban kuskure ne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan