Sharhi: Jihar Lagos na haɓaka Kano na gurguncewa

  170

  Ranar 25 GA watan Janairu 2021 kamfanin ccecc na kasar Sin, wato China ya bada sanarwar kammala aikin layin dogo, da ya hada Ibadan da Lagos, sannan kuma ya hada Lagos din da tashar jirgin ruwa ta Apapa.

  Wannan layin dogo shi ne ginshikin da zai hade layin dogon da ya taso daga Ibadan sai ya tuke da Apapa Port daga tashar Mobolaji Johnson zuwa Ebute Metta ya wuce har gindin ruwa. Wannan layin kilomita takwas ne da rabi. Injiniyoyin China da MInistan sufuri Rotimi Amechi suna farin ciki.

  Da kammala wannan aikin, an sallami harkar sufuri ta kasa a yankunan Yarabawa. Lagos da Ogun da Oyo da Ondo da Ekiti, an gama biya musu bukata. Akasari ta wannan tasha ake shigo wa da kaya Najeriya, ta nan ake fitar da su kasashen ketare.

  An kara wa Lagos karfin kasuwanci da hanyoyi na samun kudi da gina wa daidaiku da kamfanoni madogarar tattalin arziki. Kano kuwa cibiyar kasuwanci a arewa ko oho! A yanzu kudin da ake sarrafawa a tashar Apapa kadai, ya kai tiriliyan uku a shekara. A bara tsabar jarin da yan kasuwar waje suka shigo da shi Najeriya kusan Dala biliyan biyu a Lagos ya tsaya. Kwata-kwata Dala dubu 250 ne ya zo Kano ta amfana.

  An yi titin jirgin kasa na gani na fada, dan zamani daga Ibadan zuwa Lagos. Tsawon layin dogon ya kai kilomita 156, kamar a ce a kwatance daga Kano zuwa Zariya ne. An kashe kudi kusan dala biliyan goma. An gama komai, sai sharbar romon dimokuraddiya.

  Matsalar da tafi damun arewa, ita ce harkar tsaro. Idan ba tsaro, ba zaman lafiya, babu ba aminci, maganar kasuwanci. A bisa lissafin NBS wato hukumar kididdiga ta kasa na bara an yi kidnafin a arewa sau 2454, a kudu kuma sau 406. Haka kuma, a bara an kashe mutane 914 a jihohin kudu guda 16, a jihohin arewa kuma an kashe mutum 6803.

  Lokacin tashi tsaye fa yana neman kure wa, da zarar mun shiga shekara ta 2022 maganar siyasa kara bunkasa za ta yi, a arewa da Kano an sha mu basilla. Ina wadanda muka zaba suke, Pls?

  Bello Muhammad Sharada, ya rubuto daga Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan