Amfani Da Shugabannin Al’umma Zai Taimaka Wajen Magance Rikicin Boko Haram— CITAD

130

Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma, CITAD, ta bayyana cewa yin amfani da shugabannin al’umma zai taka rawa sosai wajen magance rikicin Boko Haram da ake fama da shi a shiyyar Arewa Maso Gabashin Najeriya.

CITAD ta ce ta gano hakan ne bayan da ta gudanar da wani bincike a yankin Arewa Maso Gabashin ƙasar nan, inda sakamakon binciken ya nuna cewa yin amfani da shugabannin al’umma da na addinai da na matasa da kuma shugabannin ƙungiyoyin mata zai taimaka sosai wajen magance wutar rikicin da take ƙoƙarin gagarar Kundila.

Babban Jami’in Gudanar da Shirye-Shirye na CITAD, Malam Isah Garba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gudanar da wata maƙala da aka gabatar mai taken: “Hanyoyin Da Za A Bi Wajen Magance Ƙalubalen Tsaro A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya”

Malam Isah ya ce amfani da jami’an tsaro na sa ka kai da aka fi sani da Civilian JTF zai taimaka sosai wajen daƙile wutar rikicin.

Rikicin Boko Haram dai ya ɗauki tsawon shekaru fiye da 10 a yankin jihohin Maiduguri da Yobe da kuma Adamawa, inda aka samu asarar dubban rayukan al’umma da dukiyoyi na miliyoyin naira tare da samar da dubban ‘yan gudun hijira.

Taron dai ya samu halarcin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, AIG Habu Sani, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Uzairu Muhammad, da Babban Kwamandan Rundunar Civil Defense da kuma Ƙungiyoyin Fararen Hula, CSOs daga ciki da wajen jihar Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan