Malamai sun fara nuna goyon bayan su akan matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka akan Abduljabbar

170

Awanni kaɗan da matakin gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na haramtawa fitaccen malamin addinin Islama na jihar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa’azi a dukkanin faɗin jihar nan take, malamai a Kano da wasu sassan arewacin Najeriya sun fara nuna goyon bayan su akan wannan matakin da gwamnatin Kanon ta ɗauka.

Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo, ɗaya daga cikin fitattun malamai ne a jihar Kano ya bayyana godiya ga Allah da kuma gwamnatin jihar Kano, akan wannan mataki da ta ɗauka. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a safiyar yau Alhamis.

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Sannan godiya ga Gwamnatin Kano a kan wannan mataki da ta dauka a kan mai zagin Annabi S.A.W da sahabbansa

Allah ya sa wannan ya zama sababin shiriyarsa da al’ummar da ya batar. Ameen” In ji Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo

Shi ma fitaccen malamin addinin musuluncin nan na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar Sokoto, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, ya bayyana jin daɗinsa akan matakin da gwamnatin Ganduje ta ɗauka akan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ɗin, ya ce abu na gaba kuma da ya kamata shi ne gwamnatin Kano ta tilasta Abduljabbar ɗin zama da malaman Kano domin tattaunawa a tsakaninsu.

Matakin da gwamnatin Kano ta dauka a kan Abduljabbar ya yi kyau. Abin da ya fi shi kyau bayan haka shi ne a tilasta shi zaunawa da Malaman Kano su tattauna a bainar jama’a. Allah ya kare mu daga fitina a addininmu” In ji Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto

Shi kuwa limamin masallacin juma’a na jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudil a jihar Kano, Farfesa Auwal Ibrahim Magashi addu’a ya yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan wannan mataki da ya ɗaya.

Hadimul Islam, Allah ya tabbatar da kai bisa abinda yake so ya yarda dashi” In ji Farfesa Auwal Ibrahim Magashi

A jiya ne dai majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramtawa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa’azi a dukkanin faɗin jihar Kano, sakamakon yin kalaman da za su iya haifar da tarzoma a lokacin da ya ke yin wa’azi.

Haka a baya an samu takun-saka tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu malaman jihar Kano wadanda suke ganin yana yin kalaman da suka saɓawa addinin Musulunci, sai dai ya sha musanta wannan zargi inda ya ce galibin abubuwan da yake faɗa ya samo su ne a littafan Musulunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan