Siyasa ce ta sanya gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta min yin wa’azi – Abduljabbar Nasiru Kabara

148

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya mayar da martani ga matakin da Gwamnatin jihar Kano ta dauka a ranar Laraba, na hana shi yin Wa’azi da dukkanin wasu tarurrukan Addini a fadin jihar.

Abduljabbar Kabara ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanya siyasa ne wajen daukar wancan mataki.

Malamin yana mayar da martanin ne a yayin wata hira da gidan Jaridar Daily Trust yayi dashi.

Ya ce saboda ya yaki takarar Ganduje a zaben 2019 ne, ya sanya gwamnatin daukar wancan mataki, inda ya ce kwata-kwata ba a yi Masa adalci ba.

Sheikh Abduljabbar ya ce shi mai bin doka da oda ne, a don haka yayi kira ga magoya bayan sa da suyi hakuri akan matakin da Gwamnatin ta dauka.

“Tuni na fadawa magoya baya na su adana kuri’un su, domin daukar matakin daya dace a zabe na gaba” a cewar Abduljabbar.

Idan za’a iya tunawa, a ranar Laraba ne Majalisar Zartarwa ta jihar Kano, ta bakin Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammadu Garba, ta dauki matakin hana Malam Abduljabbar Kabara gudanar da duk wani taro na Addini a fadin jihar Kano, inda Gwamnati ta ce ta dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan