Babu wanda ya rushe ginin Makarantar Abduljabbar – Ustaz Yasir Ramadan Gwale

144

Wasu kafafen yada labarai sun bayar da wani labarin da ba gaskiya ba, inda suka bayyana cewar an rushe makaranta mallakar Abduljabbar da ake kira As’habul Kahfi, wannan zance ba gaskiya bane, domin kuwa ginin Makarantar na nan a tsaye.

Duk hotunan da ake yadawa wasu gine gine ne da aka rushe su a Filin Mushe. Wadannan gine gine, wadan da tun usuli mutane suna zargin ko Abduljabbar na da hannu a wadannan gine gine, inda shi Abduljabbar din yayi niyyar mamayewa ta hanyar gudanar da karatuttukansa a wajen maimakon cikin Masallacin sa da harabarsa da yake Sallah, amma sai yaki karatu acan ya fito Filin Mushe yana karatu a filin Allah.

Abduljabbar yayi niyyar mamaye Filin ta hanyar sanya turakun fitilu da suke haska wajen, abinda yake nuna yana son mamaye wajen. To, daga bisani kuma aka wayi gari an siyarwa da wasu wannan fili inda suka fara ginawa, wasu da yawa bisa rashin sani, sai suka yi zaton ko yaran Abduljabbar ne suke gine ginen, wanda a zahiri shi kansa Abduljabbar bai so gine ginen ba saboda yana son mallake wajen, anyi ta yada jita jita da rade radi cewar ya hada kai da wasu ma’aikatan Gwamnati da zasu mallaka masa wajen.

To, yau kuma, aka wayi gari ana rushe rushen gine ginen da aka fara a cikin wannan fili. Su kuma wasu kafafen yada labarai ba a gaya musu rahoton gaskiya ba, kawai suka bada sanarwar wai ana rusawa Abduljabbar Makaranta, wanda sam ba haka bane, makarantarsa na nan a inda take babu wanda ya rushe ta. Yana da kyau labari irin wannan kafafen labaru su tabbatar da sahihancinsa kafin su yada.

Wadannan hotuna da ake yadawa sam ba makarantar Abduljabbar bane, sune gine ginen da aka fara yi a filin. Allah ya yi mana maganin fitintinu da masu son tayar da su. Gwamnan Kano kuma na cikin addu’o’in mu na alheri, Allah ya cigaba da dafa masa wajen yin abinda ya dace game da wannan waje.

Daga shafin Yasir Ramadan Gwale

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan