Home / Labarai / Hotuna: Buba Galadima ya yi bikin cika shekaru 73 da haihuwa

Hotuna: Buba Galadima ya yi bikin cika shekaru 73 da haihuwa

Jagoran ‘yan jam’iyyar APC da suka ware daga uwar jam’iyyar Injiniya Buba Galadima, ya yi bikin cika shekaru 73 da haihuwa.

Injiniya Buba Galadima tare da iyalinsa

Buba Galadima wanda fitaccen ɗan siyasa ne, ya yi bikin ne tare da iyalinsa a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Taƙaitaccen Tarihin Buba Galadima

An haifi Injiniya Buba Galadima a lardin Gashua da ke jihar Yobe a yanzu haka, a cikin shekarar 1948.

Ya fara makaranta a wani kauye da ake kira Bizzi a shekarar 1959. A shekarar 1961 kuma ya koma Gashua inda ya kammala karatu a 1965 sannan ya tafi makarantar sakandare ta Provincial da ke Maiduguri a jihar Borno a 1966 zuwa 1970.

Injiniya Buba Galadima ya samu nasarar shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya yi karatu a makarantar share fage (School of Basic Studies) inda ya fara rike shugabancin shugaban dalibai na makarantar.

Ya yi karatun digirinsa na farko a fannin injiniya na gine-ginen gidaje da hanya a shekarar 1975.

Haka kuma Injiniya Buba Galadima ya shiga siyasa ne a cikin shekarar 1978.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *