Inda Da Rai Da Rabo: Bola Tinubu ya sabunta rijistarsa ta APC

153

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake yin rijistar jam’iyya da kuma sabunta zamansa mamba a jam’iyyarsa APC a jihar Lagos.

Masu taimaka masa kan harakokin watsa labarai sun nuna hotunan yadda shugaban ya sabunta rijistar a shafin facebook.

Bola Tinubu a lokacin da ya ke sabunta rijistar jam’iyyar sa ta APC


Jam’iyyar APC dai ta kafu ne bayan jam’iyyun AC da CPC da ANPP da wani bangare na APGA sun dunkule kafin a shiga babban zaben 2015, abin da ya sa suka kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP da dan takararta Shugaba Goodluck Jonathan.

Ana ganin Bola Ahmed Tinubu yana daga cikin waɗanda za su nemi kujerar shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar 2023.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan