Home / Lafiya / Za Mu Fara Sa Ƙafar Wando Ɗaya Da Waɗanda Ba Sa Sa Takunkumin Rufe Fuska—KAROTA

Za Mu Fara Sa Ƙafar Wando Ɗaya Da Waɗanda Ba Sa Sa Takunkumin Rufe Fuska—KAROTA

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ya yi kira ga al’ummar jihar cewa kowa ya mallaki takunkumin rufe fuska.

Shugaban na KAROTA ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Juma’a.

Baffa ya ce jami’an KAROTA sun shirya tsaf domin fara kama duk mutumin da aka samu ya fito ba tare da takunkumin ba, tare da gurfanar da shi a gaban kotun tafi-da-gidanka

“Masu rake, lemo, ayaba, kwakwa, yalo, gyaɗa da sauransu, duk wanda muka samu ba shi da takunkumi zamu kama shi mu miƙa shi gaban kotu”, in ji Baffa, kamar yadda jaridar Alƙibla ta rawaito.

About Hassan Hamza

Check Also

Yin ƙarin gashin idanu hatsari ne ga lafiyar ido

Animashaun ta ce gashin ido na asali yana kare idanu daga tarkace, ƙura da ƙananan ƙwayoyin cuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *