Home / Addini / Ba Za Mu Bari Abduljabbar Ya Yi Mana Irin Abin Da El-zakzaky Ke Yi A Zariya Ba— Ganduje

Ba Za Mu Bari Abduljabbar Ya Yi Mana Irin Abin Da El-zakzaky Ke Yi A Zariya Ba— Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ba za ta ƙyale marasa fahimtar addini su ƙara haifar da wani sabon rikici a jihar ba.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa malaman addinin Musulunci jawabi a Fadar Gwamnatin Jihar.

Gwamna Ganduje ya kira malaman zuwa Fadar Gwamnatin Jihar ne biyo bayan hana Abduljabbar Nasiru Kabara wa’azi a dukkan faɗin jihar, sakamakon zargin sa da yunƙurin tunzura jama’a.

Gwamnan ya tuna irin tashin-tashinar da rikicin Maitatsine ya haifar a jihar Kano, ya kuma yi jawabi kan yadda mummunar fahimtar addini ta haifar da rikicin Boko Haram a Maiduguri.

Aikace-aikacen mabiya Muhammad Marwa, wani malami ɗan Kamaru da ya zauna a Kano da aka fi sani da Maitatsine, su suka haifar da rikicin Maitatsine a shekarun 1979 zuwa 1980.

Fiye da mutane 5000 aka yi amannar sun mutu a rikicin, da suka haɗa har da shi kansa Maitatsine, jami’an ‘yan sanda da sojoji da dama.

“A Kano, ba za mu bari a sake maimaita rikicin Maitatsine ba, kuma ba za mu ɗauki barazanar Kabara da wasa ba kamar yadda aka yi da abokinsa a Zariya”, Gwamna Ganduje ya bayyana haka a wata magana dake nuna yana nuni ne ga Ibrahim El-zakzaky, Shugaban Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, da aka fi sani da Shi’a, wanda yake a tsare a hannun hukumomin Najeriya.

About Hassan Hamza

Check Also

Ilimi Kogi: Kasuwancin Cryptocurrency Haramun ne – Sheikh Muhammad Bn Usman

Babban limanin masallacin juma’a na Sahaba da ke nan Kano Sheik Muhammad Bin Usman ya …

4 comments

  1. Allah yasaka da alkhairi Uban Abba.
    Madala da wannan hobasa.👍🙏

  2. Wannan yayi dai dai gwamna ganduje HK akeson shugaba jajir tacce Allah y kara daukaka

  3. Allah ya kyauta. Kuma haka ake son shugaba da hangen nesa akan duk abinda zai iya janyo fitina ka can gaba sai ayi maganinsa tunda wuri.
    Allah ya kara lafiya Uban Abba

  4. Hon Bello salisu chafe

    Allah kanisantamu da makiyanmu duniya da lahira

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *