Ba Za Mu Bari Abduljabbar Ya Yi Mana Irin Abin Da El-zakzaky Ke Yi A Zariya Ba— Ganduje

105

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ba za ta ƙyale marasa fahimtar addini su ƙara haifar da wani sabon rikici a jihar ba.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa malaman addinin Musulunci jawabi a Fadar Gwamnatin Jihar.

Gwamna Ganduje ya kira malaman zuwa Fadar Gwamnatin Jihar ne biyo bayan hana Abduljabbar Nasiru Kabara wa’azi a dukkan faɗin jihar, sakamakon zargin sa da yunƙurin tunzura jama’a.

Gwamnan ya tuna irin tashin-tashinar da rikicin Maitatsine ya haifar a jihar Kano, ya kuma yi jawabi kan yadda mummunar fahimtar addini ta haifar da rikicin Boko Haram a Maiduguri.

Aikace-aikacen mabiya Muhammad Marwa, wani malami ɗan Kamaru da ya zauna a Kano da aka fi sani da Maitatsine, su suka haifar da rikicin Maitatsine a shekarun 1979 zuwa 1980.

Fiye da mutane 5000 aka yi amannar sun mutu a rikicin, da suka haɗa har da shi kansa Maitatsine, jami’an ‘yan sanda da sojoji da dama.

“A Kano, ba za mu bari a sake maimaita rikicin Maitatsine ba, kuma ba za mu ɗauki barazanar Kabara da wasa ba kamar yadda aka yi da abokinsa a Zariya”, Gwamna Ganduje ya bayyana haka a wata magana dake nuna yana nuni ne ga Ibrahim El-zakzaky, Shugaban Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, da aka fi sani da Shi’a, wanda yake a tsare a hannun hukumomin Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan