Home / Featured / Farfesa Abdallah Uba Adamu na yin adabo da shugabancin jami’ar NOUN

Farfesa Abdallah Uba Adamu na yin adabo da shugabancin jami’ar NOUN

A gobe 10 ga watan Fabrairu wa’adin shugaban jami’ar Koyo daga gida ta Najeriya, NOUN, farfesa Abdallah Uba Adamu, ya ke cika a matsayin shugaban jami’ar.

Babu shakka a lokacin shugabancin Farfesa Abdallah Uba Adamu ya samu nasarar ɗaukaka daraja da martabar jami’ar NOUN fiye yadda ya same ta.

Haka Farfesa Abdallah Uba ya yi matuƙar ƙoƙari wajen wayar da kan al’ummar Najeriya game da jami’ar ta NOUN, domin kafin zuwa sa, da yawa mutanen ƙasar nan ba su ma san yadda tsarin karatun NOUN yake ba. Domin hatta su kansu hukumomin da ke sa ido a kan jami’ar, ba su fahimce tsarin sosai ba. Domin a da sun ɗauka wani karatu ne na je-ka-na-yi-ka, amma abin ba haka yake ba.

A yanzu haka dai jami’ar NOUN ta tashi daga tsohon yanayin da ta ke ciki, a halin da ake ciki komai yanzu da intanet ake gudanarwa. A yanzu sai a dauke ka jami’ar ta hanyar cika fom a wayar ka kai-tsaye. Haka kuma ya kawo sabon sauyi, domin ilmi ya zama a tafin hannun mai son yin ko kuma a ce har a cikin aljihun ka, domin ba sai ka je aji ka yi zaman-dirshan ba.

Hakazalika Farfesa Abdallah Uba Adamu, ya yi nasarar dawo da cibiyar jami’ar daga jihar Legas zuwa birnin tarayya Abuja.

Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2016 ne Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama shugaban jami’ar ta NOUN.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *