Home / Lafiya / Gwamnan Borno, Zulum, Ya Gamu Da Mummunan Haɗarin Mota

Gwamnan Borno, Zulum, Ya Gamu Da Mummunan Haɗarin Mota

Ayarin motocin Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya gamu da mummunan haɗarin mota.

Wannan mummunan haɗari ya afku ne ranar Talata a lokacin da Gwamna Zulum yake dawo wa Maiduguri daga Mafa, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Wasu shaidun gani da ido sun ce haɗarin ya afku ne sakamakon fashewar tayar wata mota, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku a cikin ayarin.

Jaridar Intanet, Solacebase, ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Mai Magana da Yawun Gwamna Zulum, Isa Gusau, amma abin ya ci tura saboda wayarsa ta ƙi shiga.

About Hassan Hamza

Check Also

Ƴan Bindiga sun yi awon gaba da wasu tarin jama’a a lokacin da su ke sallar Tuhajjud a Katsina

Wasu rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa kimanin mutane arba’in da su ka haɗa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *