Gwamnatin jihar Bauchi ta mayar da sunan jami’ar Gaɗau zuwa Sa’adu Zungur

99

Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta amince da sauya sunan jami’ar jihar daga Gadau zuwa Sa’adu Zungur. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Tilde ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin tunawa da marigayi Malam Sa’adu Zungur, wanda fitaccen ɗan kishin ƙasa da gwagwarmayar ƙwato ƴancin talaka.

Wanene Malam Sa’adu Zungur?

Malam Sa’adu Zungur ya kasance shararren marubucin adabin Hausa kuma dan siyasa, ya yi gwagwarmaya wajen yaki da yadda turawan mulkin mallaka suka mulki Najeriya a wancan zamanin. Malam Sa’adu ya kasance mai kaifin basira, hazaka da hangen nesa.

Marigayi Malam Sa’adu Zungur

An haifi Sa’adu Zungur a watan Nuwamban shekarar 1914 a cikin garin Bauchi. Bayan yi yi karatun Islamiya da kuma na littafafan addinin musulunci, malam ya halarci Yaba College da ke birnin Legas a shekarar 1934.

Bayan dawowar sa daga birnin Legas, Malam Sa’adu Zungur ya kasance malamin makaranta a cikin garin Zariya. Lokacin zaman sa a garin Zariyan kuma ya kirkiro kungiyar Zaria Friendly Society tare da Malam Abubakar Imam da wasu abokansu a wancan lokacin. Kungiyar tasu wacce daga baya ta kasance kamar kungiyar siyasa a yankin ta sha suka daga wasu Sarakunan lokacin.

A shekarar 1942 ya dawo garin Bauchi in da ya ci gaba da harkar karantarwa. Bayan gamayya da suka yi da su Malam Aminu Kano da Muhammad Baba Halla na yin gwagwarmaya da yadda ake mulki a yankin Arewa a wancan zamanin, Malam Sa’adu Zungur ya kasance sakataren jam’iyar NCNC a shekarar 1948.

Malam Sa’adu Zungur ya yi rubuce-rubuce da dama a fannin adabin Hausa. Wasu daga cikin litattafan da ya rubuta wanda suka shahara sun hada da:

Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya
Maraba Da Soja


Malam Sa’adu Zungur ya kasance abun koyi ga wasu marubutan adabin Hausa irin su Malam Abubakar Ladan Zariya da sauran ma rubuta.

Allah ya yiwa Malam Sa’adu Zungur rasuwa a shekarar 1958 a cikin garin Bauchi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan