Rushe gadar sama ta ƙofar Nasarawa aika – aika ne kuma awon igiya ne – Jafar Sani Bello

213

Fitaccen ɗan siyasar nan kuma wanda ya taɓa neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekara 2015 Jafar Sani Bello ya bayyana ƙudurin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar sama ta ƙofar Nasarawa a matsayin aika – aika kuma awon igiya.

Jafar Sani Bello wanda ya yi shuhura wajen yin adawa da salon mulkin jam’iyyar APC tare da sukar manufofin shugaba Muhammad Buhari, ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a matsayin martani ga shirin gwamnatin jihar Kano na rushe gadar saman.

“Rushe gadar Kofar Nassarawa Yanzu aika-aika ne, awon Igiya” In ji Jafar Sani Bello

Wannan dai yana zuwa a dai-dai lokacin da al’ummar jihar Kano ke bayyana ra’ayoyinsu tare da kafsa muhawara akan shirin gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na shirin rushe gadar.

Me Gwamnatin Jihar Kano Ta Ce Akan Rushe Gadar Sama Ta Kofar Nassarawa?

Gwamantin Kano ta ce akwai yiwurar rushe gadar sama ta kofar Nassrawa sakamakon zaizayerar da gadar ta fara yi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammdu Garba ne ya sanar da hakan lokacin da ya ke karɓar baƙuncin wata ƙungiyar siyasa mai taken ‘Ganduje Raya Kano Yake’.

Malam Muhammd Garba ya ce tuni suka shiga nazari tare da ƙwararru kan irin matsalolin da gadar ke haifarwa ga al’ummar jihar Kano. Ya ƙara da cewa sun lura da gadar ta fara zaizayewa saboda rashin kyawu da ingancin aikin da a ka yi.

Haka kuma Malam Muhammad Garba ya ce da zarar ƙwararru sun gama nazari a kai gwamnatin jihar Kano za ta duba yiwuwar rushe gadar tare da sake ta.

A ƙarshe kwamishinan ya ce ayyukan gwamnatin baya ayyuka ne marasa kan gado waɗanda ba a yi amfani da ilimi ba wajen aiwatar da su.

Turawa Abokai

2 Sako

  1. I’m now not certain the place you’re getting your info,
    however great topic. I needs to spend some time learning much more
    or working out more. Thanks for fantastic information I was in search of this info for my
    mission.

  2. Hi, I do believe this is an excellent blog. I stumbledupon it 😉 I will come back yet again since
    I book-marked it. Money and freedom is the best way to change, may you be rich and continue to guide others.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan