Ba Rabo Da Gwani Ba: Shekaru 45 da yiwa Janar Murtala kisan gilla

159

A wannan Asabar ɗin ake bikin cikar shekaru 45 da kisan gillar da aka yi wa Janar Murtala Ramat Muhammad, tsohon shugaban mulkin soji na Tarayyar Najeriya.

Janar Murtala Muhammad shi ne ake wa kallon shugaba mai gaskiya da aka taba samu a Najeriya wanda ya yi kokarin girka gaskiya da adalci tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.

Janar Murtala Muhammad shi ne ake wa kallon shugaba mai gaskiya da aka taba samu a Najeriya wanda ya yi kokarin girka gaskiya da adalci tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.

Tun bayan mutuwarsa a ranar 13 ga watan Fabrairu, wasu kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin dalibai da tsoffin ma’aikata a Najeriya ke ware wannan rana domin juyayin mutuwar shi tare da gudanar da taro domin gabatar da kasidu game da rawar da shugaban ya taka a ci gaban Najeriya.

Janar Murtala Muhammad shi ne shugaban da ake wa kallon ya samar da tsare tsare masu inganci a Najeriya, wanda ya bada damar samar da gwamnatin farar hula a kasar.
Wani abu da ake mutunta Obasanjo wanda ya gaje shi ne yadda ya aiwatar da ayyukan da shugaban ya kudurta gudanarwa a Najeriya.

A lokacin da mulkin Obasanjo tare da makaranban shi a Gwamnati, da suka hada da shehu Musa Yar’adua da TY Danjuma da IBB da Domkat Bali sun yi kokarin ganin sun aiwatar da ayyukuna da Murtala ya kudurta gudanarwa a Najeriya.

Saboda kima da martabar Janar Murtala Muhammad ne a Najeriya, aka saka hotonsa cikin kakin Soji a kudin kasar nan Naira Ashirin.

Takaitaccen tarihin Janar Murtala Mohammad

An haifi janar Murtala Ramat Muhammed ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya yi karatu a kwalejin Barewa dake Zaria.

A shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda yayi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy ta Sandhurst dake Burtaniya.

Janar Mutala ya samu mukamin Laftanal a shekarar 1961.

Gabanin komawarsa Najeriya a shekarar 1962, ya je rangadin aiki a kasar Congo a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya.

A shekarar 1964 ya ka bashi mukamin Manjo na wucin gadi, bayan da aka bashi ragamar kula da sashin sadarwa a hedkwatar rundunar soji ta Kaduna.

Janar Murtala ya koma Lagos inda ya zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a lokacin da aka bashi ministan tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da akai juyin mulki na farko a shekarar 1966.

Shugaban kasa manjo janar Aguiyi-Ironsi ya kara masa girma zuwa Laftanal Kanal koda yake shima na wucin gadi ne, a watan Afrailun shekarar 1966.Bayan juyin mulki na farko, sau uku janar Murtala ke neman hada kan sojojin arewa dake Lagos domin ayi juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunkuri bai yi nasara ba bisa harbe wasu sojoji da akayi a Abeokuta.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yakin basasar da akai a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin Biafra daga Najeriya.

A wannan lakacin janar Murtala ya jagoranci rundunar sojin da suka murkushe sojojin Biafra tare da kawo karshen yaki basasar baki daya kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Yana matsayin birgediya ne sojojin da sukayi juyin mulki na uku a Najeriya suka nada Murtala a matsayin shugaban kasa , inda a watan Janairun shekarar 1976 aka kara masa girma zuwa janar mai anini hudu, wato kololuwa kenan.

Har ila yau a wannan lokaci ne janar Murtala ya kirkiro da sabbin jahohi 7 ya kuma bayyana bukatar mayarda babban birnin Najeriya zuwa Abuja da kuma alkawarin mika mulki ga fararen hula a shekarar 1979.

To masu iya magana kance kana taka Allah na nashi, ranar 13 ga watan Fabrerun sojoji karkashin jagorancin Dimka sukayi yunkurin kifar da gwamnatin sa yunkurin da bai nasara ba, illa dai kashe-kashen da akayi, inda suka budewa motar janar Murtala Ramat Muhammed wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofis.

Bayan mutuwarsa an nada mataimakinsa laftanar janar Obasanjo a matsayin shugaban kasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan