Ba A Fara Rijistar Jarrabawar UTME Ta 2021 Ba— JAMB

98

Hukumar Shiriya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire, JAMB, ta ce har yanzu ba ta tsayar da ranar da za ta fara yi wa ɗalibai rijistar Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire ta Bai Ɗaya, wato UTME, ta 2021 ba.

JAMB ta bayyan haka ne ranar Talata a cikin wata sanarwa da Jami’inta na Huɗɗa da Jama’a, Dakta Benjamin Fabian ya fitar.

JAMB ta shawarci jama’a da su yi watsi da wani asusun bogi na Twitter wanda ya sanar da fara rijistar jarrabawar.

A wani ɓangaren kuma, a ranar Lahadi ne JAMB ta ce zuwa 15 ga Yuni, 2021, za a kammala bayar da guraben karatu na shekarar karatu ta 2020/2021.

JAMB ta ce an ɗauki wannan matakin ne a wani taro da aka yi ta Intanet da shugabannin manyan makarantun gaba da sakandire ranar Laraba, 24 ga Fabrairu, 2021.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan