Ba Zan Shiga Muƙabalar Da Za A Yi Da Abduljabbar Ba— Sarkin Musulmi

118

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa babu buƙatar yin muhawara da Abduljabbar Nasiru Kabara, duba da irin kalaman da yake yi.

Sarkin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Ƙungiyar Jama’atun Nasril Islam, JNI, da yake jagoranta ta fitar ta hannun sakatarenta, Dakta Khalid Abubakar Aliyu.
JNI ta ce a baya ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakin da ta ɗauka na dakatar da Abduljabbar daga gudanar da karatuttuka tare da rufe masallacinsa.

Ƙungiyar ta ce ba za ta shiga duk wata tattaunawa da za a shirya da Abduljabbar ba.

Tuni dai Gwamnatin Jihar Kano ta tsayar da Lahadi, 7 ga Maris, 2021, a matsayin ranar da za a yi muƙabala da Abduljabbar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan