Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Shirya Muƙabala Da Abduljabbar

142

Kotun Majistire Mai Lamba 12, Gidan Murtal, Jihar Kano, ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano shirya muƙabala tsakanin Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman Kano.

Wannan dakatarwa ta biyo bayan ƙarar da wani lauya, Barista Ma’aruf Yakasai ya shigar, inda ya roƙi kotun da ta dakatar da muƙabalar
.
Mai Shari’a Mahmud Jibril ne ya jagoranci zama kotun, inda ya dakatar da shirya muƙabalar daga nan har zuwa 22 ga Maris, 2021.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan