Zan Yi Biyayya Ga Umarnin Kotu Na Dakatar Da Muƙabala— Ganduje

133

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai yi biyayya ga umarnin da kotu ta bayar na dakatar da muƙabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawal.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Kano mai biyayya ce ga umarnin kotu, a don haka za ta yi biyayya, musamman duba da kotun tana da hurumin bada wannan umarni.

Ya ƙara da cewa ba daidai ba ne kotu ta bada umarni gwamnati kuma ta yi ƙememe, saboda haka a yanzu babu maganar muƙabala ranar Lahadi mai zuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan