Haɗin Kan Al’ummar Kogi Ne Ya Dame Ni Ba COVID-19 Ba— Gwamnan Kogi

102

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce ba zai miƙa kai a yi masa riga-kafin COVID-19 ba.

A mako mai kamawa ne ake sa ran gwamnonin Najeriya za su karɓi riga-kafin na COVID-19 samfurin AstraZeneca/Oxford COVID-19.

Gwamna Bello ya bayyana haka ne a Gidan Talabijin na Channels a cikin shirin ‘Politics Today’.

Ya kuma ce ba wata cuta da take damun sa, kuma ba zai bari a yi amfani da al’ummar jihar a matsayin zakaran gwajin dafi ba.

“Ba COVID-19 ba ce matsalarmu a jihar Kogi. Muna da batutuwa da al’amura da yawa masu muhimmanci da muke mayar da hankali a kai a jihar Kogi. Rashin tsaro da muka samu, mun fuskance shi da sauran abubuwa. Rashin haɗin kai da muka samu a ƙasa kuma mun haɗa kan jihar Kogi a yau, ba COVID-19 ba.

“COVID-19 ɗan ƙanƙanin abin da muke mayar da hankali ne a jihar Kogi; an samu ɓarkewar Zazzaɓin Lassa da Zazzaɓin Cizon Sauro, kuma an kawo ƙarshen waɗannan abubuwa ba tare da wani surutu ba”, in ji Gwamnan na Kogi.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne Najeriya ta karɓi ƙwayoyin riga-kafin COVID-19 samfurin AstraZeneca/Oxford COVID-19 har miliyan huɗu.

An shigo da ƙwayoyin riga-kafin ne ta Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikw, Abuja.

Tuni wasu ma’aikatan lafiya suka karɓi riga-kafin.

Mutum na farko da ya karɓi riga-kafin shi ne Dakta Cyprian Ngong, mai aiki a Babban Asibitin Ƙasa, Abuja.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa na Yaƙi da COVID-19, Boss Mustapha, shi ya ƙaddamar da shirin bada riga-kafin a Abuja ranar Juma’a.

A yau Asabar ne ake sa ran Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo za su karɓi tasu riga-kafin domin gamsar da ‘yan Najeriya su ma su karɓa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan