Kwankwaso Ya Halarci Ɗaurin Aure Ba Tare Da Jar Hula Ba

122

Tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya halarci bikin iyalan Kwamishiniyar Ruwa ta Jihar Ribas, kuma Shugabar Ɗarikar Kwankwasiyya ta Jihar Godwin Ettah, da kuma Humphrey Nzeribe.

Ango shi ne Nyein Ettah, amaryar kuma ita ce Ifeanyi Nzeribe.

An yi wannan biki ne a Cocin West African Peoples’ Institute, WAPI Sport Field, Calabar, Jihar Ribas.

Mai Taimaka Wa Kwankwaso Kan Kafafen Watsa Labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana haka a shafin Facebook.

Ba kasafai dai ake ganin tsohon Sanatan ba tare da har hula ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan